|
| 1 |
|
| Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah. |
|
| 2 |
|
| Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.” |
|
| 3 |
|
| Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set. |
|
| 4 |
|
| Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
|
| 5 |
|
| Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu. |
|
| 6 |
|
| Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh. |
|
| 7 |
|
| Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
|
| 8 |
|
| Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu. |
|
| 9 |
|
| Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan. |
|
| 10 |
|
| Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
|
| 11 |
|
| Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu. |
|
| 12 |
|
| Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel. |
|
| 13 |
|
| Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata |
|
| 14 |
|
| Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu. |
|
| 15 |
|
| Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared. |
|
| 16 |
|
| Bayan ya haifi Yared, Mahalalel ya yi shekara 830, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata |
|
| 17 |
|
| Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu. |
|
| 18 |
|
| Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok. |
|
| 19 |
|
| Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
|
| 20 |
|
| Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu. |
|
| 21 |
|
| Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela. |
|
| 22 |
|
| Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
|
| 23 |
|
| Gaba ɗaya dai, Enok ya yi shekaru 365. |
|
| 24 |
|
| Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi. |
|
| 25 |
|
| Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek. |
|
| 26 |
|
| Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782, ya kuma haifi waɗansu ’ya’ya maza da mata. |
|
| 27 |
|
| Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu. |
|
| 28 |
|
| Sa’ad da Lamek ya yi shekara 182, sai ya haifi ɗa. |
|
| 29 |
|
| Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.” |
|
| 30 |
|
| Bayan an haifi Nuhu, Lamek ya yi shekara 595, yana kuma da ’ya’ya maza da mata. |
|
| 31 |
|
| Gaba ɗaya dai, Lamek ya yi shekaru 777, sa’an nan ya mutu. |
|
| 32 |
|
| Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet. |
|
|
|
|