Sulemanu ya gama kai da Fir'auna, Sarkin Masar, ta wurin aure, domin ya auri 'yar Fir'auna, ya kawo ta birnin Dawuda kafin ya gama ginin gidan kansa, da Haikalin Ubangiji, da garun Urushalima.
Sulemanu ya amsa ya ce, “Kai ne kake nuna ƙauna mai girma a koyaushe ga bawanka Dawuda, tsohona,domin ya yi tafiya a gabanka da aminci, da adalci, da tawali'u. Kai kuwa ka tabbatar masa da wannan ƙauna mai girma, ka kuma ba shi ɗa wanda zai hau gadon sarautarsa a wannan rana.
Domin haka ka ba ni hikima ta yi wa jama'arka shari'a, domin in rarrabe tsakanin nagarta da mugunta, gama wane ni in iya mallakar jama'arka mai yawa haka?”
Ya kuma ce masa. “Da yake ka roƙi wannan, ba ka roƙar wa kanka yawan kwanaki, ko wadata ba, ko kuma ran maƙiyanka, amma ka roƙa a ba ka hikima yadda za ka mallaki jama'a,
Da Sulemanu ya farka, ashe, mafarki ne, Sa'an nan ya zo Urushalima, ya tafi ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Ya miƙa hadayu na ƙonawa, da hadayu na salama. Ya kuma yi wa dukan barorinsa biki.
Amma ɗaya matar ta ce, “A'a, mai ran shi ne nawa, mataccen kuwa shi ne naki!” Sai ta fari ta ce, “A'a, mataccen shi ne naki, mai rai ne nawa!” Haka suka yi ta gardama a gaban sarki.
Saboda zuciyar mahaifiyar ta ainihi ta cika da juyayin ɗanta, ta ce wa sarki, “Ranka ya daɗe kada a kashe yaron! A ba ta!” Amma ɗayar ta ce, “Kada a ba kowa daga cikinmu, a ci gaba a raba shi.”
Sa'ad da dukan mutanen Isra'ila suka ji shari'ar da sarki ya yanke, sai suka girmama shi ƙwarai, gama sun gane Allah ya ba shi hikimar daidaita husuma sosai.