A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra'ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji.
Fāɗin ɗakuna na ƙasa kamu biyar ne. Fāɗin ɗakunan hawa na biyu kamu shida ne. Fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa kamu bakwai ne. Bangaye a ƙasa sun fi na saman kauri, don ɗakunan su zauna sosai, ba tare da an kafa ginshiƙai a cikin ɗakunan ba.
An gina Haikalin da duwatsun da aka sassaka tun daga can wurin da aka haƙo su, don haka ba a ji amon guduma, ko na gatari, ko na wani kayan aiki irin na ƙarfe ba, sa'ad da ake ginin Haikalin.
Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi can ƙuryar Haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne, an manne masa katakan itacen al'ul tun daga ƙasa har sama.
Katakan itacen al'ul na cikin Haikalin, an yi musu zāne mai fasalin gora da na furanni buɗaɗɗu. An rufe bangon daga ciki duka da itacen al'ul, har ba a ganin duwatsun ginin.
Tsawon Wuri Mafi Tsarki na can ciki kamu ashirin ne, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu ashirin. Ya dalaye shi da zinariya tsantsa. Ya kuma yi bagadensa da itacen al'ul.
Sulemanu ya dalaye cikin Haikalin da zinariya tsantsa. Ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban Wuri Mafi Tsarki na can ciki, sa'an nan ya dalaye su da zinariya.
Ya zana siffofin kerubobi, da na itatuwan dabino, da na furanni a dukan bangon Haikalin, wato bango na Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki na can ciki.
A shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Sulemanu a watan Bul, wato watan takwas, aka gama ginin Haikalin, daidai yadda aka zayyana fasalinsa. Sulemanu ya yi shekara bakwai yana ginin Haikalin.