Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Suka fa kawo akwatin alkawarin Allah, suka sa a cikin tentin da Dawuda ya kafa dominsa, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa da hadayu na salama a gaban Allah. |
| 2 |
| Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji. |
| 3 |
| Sa’an nan ya ba da dunƙulen burodi da wainar dabino da kuma kauɗar zabibi ga kowane mutumin Isra’ila namiji da ta mace. |
| 4 |
| Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila. |
| 5 |
| Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna, |
| 6 |
| Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah. |
| 7 |
| A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji. |
| 8 |
| Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi. |
| 9 |
| Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa. |
| 10 |
| Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki. |
| 11 |
| Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum. |
| 12 |
| Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata, mu’ujizansa da kuma hukuntai da ya yanke, |
| 13 |
| Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa. |
| 14 |
| Shi ne Ubangiji Allahnmu; hukuntansa suna a cikin dukan duniya. |
| 15 |
| Yakan tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu, |
| 16 |
| alkawarin da ya yi wa Ibrahim rantsuwar da ya yi ga Ishaku. |
| 17 |
| Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida, ga Isra’ila kamar madawwamin alkawari. |
| 18 |
| “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana kamar rabon da za ka gāda.” |
| 19 |
| Sa’ad da suke kima, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta, |
| 20 |
| suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga wannan mulki zuwa wancan. |
| 21 |
| Bai bar wani ya zalunce su ba; saboda su ya tsawata wa sarakuna. |
| 22 |
| “Kada ku taɓa shafaffuna; kada ku yi wa annabawana lahani.” |
| 23 |
| Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana. |
| 24 |
| Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane. |
| 25 |
| Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo; dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli. |
| 26 |
| Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ya yi sammai. |
| 27 |
| Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa. |
| 28 |
| Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai, ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji, |
| 29 |
| ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa. Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa; ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa. |
| 30 |
| Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka! Duniya ta kahu sosai; ba za tă jijjigu ba. |
| 31 |
| Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari su ce a cikin al’ummai, “ Ubangiji yana mulki!” |
| 32 |
| Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri; bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki! |
| 33 |
| Sa’an nan itatuwan jeji za su rera, za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji, gama ya zo don yă hukunta duniya. |
| 34 |
| Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne; ƙaunarsa madawwamiya ce. |
| 35 |
| Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu; tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai, don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki, don mu ɗaukaka a cikin yabonka.” |
| 36 |
| Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.” |
| 37 |
| Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana. |
| 38 |
| Ya kuma bar Obed-Edom da ’yan’uwansa sittin da takwas don su yi hidima tare. Obed-Edom ɗan Yedutun da Hosa kuma, su ne matsaran ƙofofi. |
| 39 |
| Dawuda ya bar Zadok firist da ’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon |
| 40 |
| don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila. |
| 41 |
| Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.” |
| 42 |
| Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. ’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa. |
| 43 |
| Sa’an nan dukan mutanen suka tashi, kowa ya koma gidansa, Dawuda ya koma gida yă sa wa iyalinsa albarka. |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/1chronicles/016.mp3
29
16