Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza. ’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar. |
| 2 |
| Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci. |
| 3 |
| Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima. |
| 4 |
| Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar. |
| 5 |
| Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar. |
| 6 |
| Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar. |
| 7 |
| Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib, na biyu a kan Yedahiya, |
| 8 |
| na uku a kan Harim, na huɗu a kan Seyorim, |
| 9 |
| na biyar a kan Malkiya, na shida a kan Miyamin, |
| 10 |
| na bakwai a kan Hakkoz, na takwas a kan Abiya, |
| 11 |
| na tara a kan Yeshuwa, na goma a kan Shekaniya, |
| 12 |
| na goma sha ɗaya a kan Eliyashib, na goma sha biyu a kan Yakim, |
| 13 |
| na goma sha uku a kan Huffa, na goma sha huɗu a kan Yeshebeyab, |
| 14 |
| na goma sha biyar a kan Bilga, na goma sha shida a kan Immer, |
| 15 |
| na goma sha shida a kan Hezir, na goma sha takwas a kan Haffizzez, |
| 16 |
| na goma sha tara a kan Fetahahiya, na ashirin a kan Ezekiyel, |
| 17 |
| na ashirin da ɗaya wa Yakin, na ashirin da biyu a kan Gamul, |
| 18 |
| na ashirin da uku wa Delahiya da kuma na ashirin da huɗu a kan Ma’aziya. |
| 19 |
| Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi. |
| 20 |
| Game da sauran zuriyar Lawi kuwa, Daga ’ya’yan Amram maza. Shubayel; daga ’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya. |
| 21 |
| Game da Rehabiya kuwa, daga ’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari. |
| 22 |
| Daga mutanen Izhar, Shelomot; daga ’ya’yan Shelomot maza, Yahat. |
| 23 |
| ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu. |
| 24 |
| Ɗan Uzziyel shi ne, Mika; daga ’ya’yan Mika maza, Shamir. |
| 25 |
| Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya; daga ’ya’yan Isshiya maza, Zakariya. |
| 26 |
| ’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi. Ɗan Ya’aziya shi ne, Beno. |
| 27 |
| ’Ya’yan Merari su ne, daga Ya’aziya, Beno, Shoham, Zakkur da Ibri. |
| 28 |
| Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da ’ya’ya maza. |
| 29 |
| Daga Kish, ɗan Kish shi ne, Yerameyel. |
| 30 |
| Kuma ’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot. Waɗannan su ne Lawiyawa bisa ga iyalansu. |
| 31 |
| Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda ’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane. |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/1chronicles/024.mp3
29
24