Feniyel shi ne mahaifin Gedor, Ezer kuwa shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne 'ya'yan Hur, maza, wato ɗan farin Efrata, zuriyarsa ne suka kafa Baitalami.
Yabez ya roƙi Allah na Isra'ila, ya ce, “Ka sa mini albarka, ka faɗaɗa kan iyakata, hannunka kuma ya kasance tare da ni, ka kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni.” Allah kuwa ya biya masa bukatarsa.
'Ya'yan Ezra, maza, su ne Yeter, da Mered, da Efer, da Yalon. Bitiya 'yar Fir'auna, wadda Mered ya aura, ta haifi waɗannan, Maryamu, da Shammai, da Ishaba wanda ya haifi Eshtemowa. Mered kuma ya auri wata daga kabilar Yahuza, ta haifi Yered wanda ya kafa garin Gedor. Eber kuma ya kafa garin Soko, Yekutiyel kuwa ya kafa garin Zanowa.
'Ya'yan Shela, maza, ɗan Yahuza, su ne Er wanda ya kafa garin Leka, da La'ada wanda ya kafa garin Maresha, da iyalan gidan masu aikin lilin da suke zaune a Bet-ashbeya,
da Yokim, da mutanen da suke zaune a Kozeba, da Yowash, da Saraf, waɗanda suka yi sarauta a Mowab, sa'an nan suka zauna a Baitalami. (Waɗannan labaru na tun dā ne.)
Shimai yana da 'ya'ya maza goma sha shida, da 'ya'ya mata shida, amma 'yan'uwansa ba su da 'ya'ya da yawa kamarsa. Iyalin Saminu ba su kai yawan na Yahuza ba.
Sun kuwa zauna a waɗansu wurare guda biyar, wato Itam, da Ayin, da Rimmon, da Token, da Ashan, da ƙauyukan da suke kewaye, har zuwa kudu maso gabas da garin Ba'al: Ga lissafin iyalansu da wuraren da suka zauna.
Meshobab, da Yamlek, da Yosha ɗan Amaziya, Yowel, da Yehu ɗan Yoshibiya, wato jīkan Seraiya, ɗan Asiyel, Eliyehoyenai, da Ya'akoba, da Yeshohaya, da Asaya, da Adiyel, da Yesimiyel, da Benaiya, Ziza ɗan Shifi, wato jīkan Allon, zuriyar Yedaiya, da Shimri ɗan Shemaiya.
Waɗannan da aka lasafta sunayensu, su ne suka zo a kwanakin Hezekiya Sarkin Yahuza, suka fāɗa wa alfarwai da bukkoki waɗanda suka tarar a can, suka hallaka su sarai, sa'an nan suka maye wurinsu saboda akwai makiyaya domin garkunansu a wurin.
Waɗansu daga cikinsu, mutum ɗari biyar daga zuriyar Saminu, suka tafi wajen gabashin Edom. Waɗanda suka shugabance su kuwa, su ne 'ya'yan Ishi, wato Felatiya, da Neyariya, da Refaya, da Uzziyel.