Amariya, da Malluki, da Hattush, Shekaniya, da Rehum, da Meremot, Iddo, da Ginneton, da Abaija, Miyamin, da Mawadiya, da Bilga, Shemaiya, da Yoyarib, da Yedaiya, Sallai, da Amok, da Halkiya, da Yedaiya. Waɗannan su ne shugabannin firistoci da 'yan'uwansu a zamanin Yeshuwa.
Lawiyawa su ne, Yeshuwa, da Binnuyi, da Kadmiyel, Sherebiya, da Yahuza, da Mattaniya wanda yake lura da waƙoƙin godiya, da shi da 'yan'uwansa. Bukbukiya da Unno, 'yan'uwansu, suka tsaya daura da su a taron sujada.
A zamanin Yoyakim babban firist, waɗannan su ne shugabannin iyalin firistoci, na wajen Seraiya, Meraiya ne na wajen Irmiya, Hananiya ne na wajen Ezra, Meshullam ne na wajen Amariya, Yehohanan ne na wajen Malluki, Jonatan ne na wajen Shebaniya, Yusufu ne na wajen Harim, Adana ne na wajen Merayot, Helkai ne na wajen Iddo, Zakariya ne na wajen Ginneton, Meshullam ne na wajen Abaija, Zikri ne na wajen Miniyamin da Mowadiya, Filtai ne na wajen Bilga, Shimeya ne na wajen Shemaiya, Yehonatan ne na wajen Yoyarib, Mattenai ne na wajen Yedaiya, Uzzi ne na wajen Sallai, Kallai ne na wajen Amok, Eber ne na wajen Hilkiya, Hashabiya ne na wajen Yedaiya, Netanel ne
A zamanin Eliyashib, da Yoyada, da Yohenan, da Yadduwa, Lawiyawa, har zuwa zamanin mulkin Dariyus, mutumin Farisa, aka rubuta shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa da firistoci.
Shugabannin Lawiyawa kuwa, su ne Hashabiya, da Sherebiya, da Yeshuwa, da Kadmiyel. 'Yan'uwansu suna tsaye kusa da su daki daki domin su yi yabo, su yi godiya kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta.
A lokacin keɓe garun Urushalima, sai aka nemo Lawiyawa a wurarensu duka don a kawo su Urushalima, su yi bikin keɓewa da farin ciki da godiya, da raira waƙoƙi da kuge, da garaya, da molo.
Sai na sa shugabannin Yahuza su hawo garu, sa'an nan na sa manyan ƙungiyoyi biyu waɗanda za su yi godiya, su tafi a jere. Ƙungiya guda ta bi wajen dama a kan garun zuwa Ƙofar Juji.
Sa'an nan waɗansu 'ya'yan firistoci, masu busar ƙaho, su ne Zakariya ɗan Jonatan, jīkan Shemaiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, da Mikaiya, da Zakkur, daga zuriyar Asaf.
Sauran 'yan'uwansa su ne Shemaiya, da Azarel, da Milalai, da Gilalai, da Ma'ai, da Netanel, da Yahuza, da Hanani. Suna da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗekaɗe. Ezra magatakarda ne yake gabansu.
Ƙungiyar jama'a ta biyu ta masu yin waƙoƙin godiya, ta bi ta wajen hagu. Na bi su tare da rabin jama'a a kan garu, sama da Hasumiyar Tanderu zuwa garu mai fādi,
da Kuma sama da Ƙofar, Ifraimu da wajen Tsohuwar Ƙofar, da wajen Ƙofar Kifi, da Hasumiyar Hananel, da Hasumiyar Ɗari zuwa Ƙofar Tumaki, sai suka tsaya a Ƙofar Tsaro.
Jama'a suka miƙa hadayu da yawa a wannan rana, suka yi murna, gama Allah ya faranta musu zuciya ƙwarai. Mata da yara kuma suka yi murna. Aka ji muryar murnar mutanen Urushalima daga nesa.
A ran nan aka sa mutanen da za su lura da ɗakunan ajiya, da sadakoki, da nunan fari, da zaka. Su ne za su tara nunan fari daga gonakin da suke kusa da garuruwa, bisa ga yadda doka ta ce, saboda firistoci da Lawiyawa, gama mutanen Yahuza sun yi murna saboda hidimar da firistoci da Lawiyawa suka yi.
A zamanin Zarubabel da zamanin Nehemiya dukan jama'ar Isra'ila suka biya wa mawaƙa da masu tsaron ƙofofi bukatarsu ta kowace rana. Sun kuma ba Lawiyawa sadokoki, su Lawiyawa kuma suka ba zuriyar Haruna nasu rabo.