Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Zofar ya amsa. |
| 2 |
| “Ba wanda zai amsa dukan wannan surutu? Yawan magana yakan sa mutum ya zama daidai? |
| 3 |
| Ayuba,kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba? Kana tsammani maganganunka na ba'a Za su sa mu rasa abin da za mu mayar maka? |
| 4 |
| Ka ɗauka duk abin da kake faɗa gaskiya ne, Ka kuma mai da kanka kai mai tsarki ne a gaban Allah. |
| 5 |
| Da ma Allah zai amsa maka, Ya yi magana gāba da kai, |
| 6 |
| Da ya faɗa maka hikima tana da fannoni da yawa. Akwai abubuwa waɗanda suka fi ƙarfin ganewar ɗan adam. Duba, Allah ya ƙyale wani ɓangare na laifinka. |
| 7 |
| “Kana iya gane matuƙa da iyakar Girman Allah da na ikonsa? |
| 8 |
| Sararin sama ba shi ne matuƙa a wurin Allah ba, Amma ga shi, yana can nesa da kai, Allah ya san lahira, Amma kai ba ka sani ba. |
| 9 |
| Fāɗin girman Allah ya fi duniya Ya kuma fi teku fāɗi. |
| 10 |
| Idan Allah ya kama ka ya gurfanar da kai gaban shari'a, Wa zai iya hana shi? |
| 11 |
| Allah ya san irin mutanen da ba su da amfani, Domin yana ganin dukan mugayen ayyukansu. |
| 12 |
| Idan dakikan mutane sa yi hikima, To, jakunan jeji ma sa yi irin hali na gida. |
| 13 |
| “Ayuba, ka shirya zuciyarka, Ka ɗaga hannuwanka zuwa wurin Allah. |
| 14 |
| Ka kawar da mugunta da kuskure daga gidanka. |
| 15 |
| Sa'an nan ka sāke shan ɗamarar zaman duniya, Da ƙarfi da rashin tsoro. |
| 16 |
| Duk wahalarka za ta gushe daga tunaninka, Kamar yadda rigyawa takan wuce, ba a ƙara tunawa da ita. |
| 17 |
| Ranka zai yi haske fiye da hasken rana da tsakar rana. Kwanakin ranka mafiya duhu Za su yi haske kamar ketowar alfijir. |
| 18 |
| Za ka yi zaman lafiya, cike da sa zuciya, Allah zai kiyaye ka, ya ba ka hutawa. |
| 19 |
| Ba za ka ji tsoron kowane maƙiyi ba, Mutane da yawa za su nemi taimako daga gare ka. |
| 20 |
| Amma mugaye za su dudduba ko'ina da fid da zuciya, Ba su da wata hanyar da za su kuɓuta. Sauraronsu kaɗai shi ne mutuwa.” |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/job/011.mp3
42
11