|
| 1 |
|
| “Duk abin da ka hurta, na taɓa jinsa, Na gane da shi sarai. Iyakar abin da kuka sani, ni ma na sani. Ba ku fi ni da kome ba. |
|
| 2 |
|
|
|
| 3 |
|
| Amma da Allah nake jayayya, ba da ku ba, Ina so in yi muhawara da shi a kan ƙarar da nake da ita. |
|
| 4 |
|
| Kun ɓoye jahilcinku da ƙarairayi. Kun zama kamar likitoci waɗanda ba su iya warkar da kowa ba. |
|
| 5 |
|
| Kada ku faɗi kome, Wani sai ya ce kuna da hikima! |
|
| 6 |
|
| “Ku saurara mini, zan faɗi ƙarata. |
|
| 7 |
|
| Me ya sa kuke yin ƙarya? Kuna tsammani ƙarairayinku za su taimaki Allah? |
|
| 8 |
|
| Son zuciya kuke yi, ko ba haka ba? Kuna goyon bayan Allah? Za ku goyi bayan Allah sa'ad da aka gurfanar da ni gaban shari'a? |
|
| 9 |
|
| Da Allah ya bincike ku sosai, Zai iske wani abin kirki ne a cikinku? Kuna tsammani za ku ruɗi Allah, kamar yadda kuke ruɗin mutane? |
|
| 10 |
|
| Ko da yake kun ɓoye son zuciyarku, Duk da haka zai tsauta muku, |
|
| 11 |
|
| Ikonsa kuwa zai razana ku. |
|
| 12 |
|
| Karin maganarku da muhawararku ba su da ƙarfi ƙwarai. |
|
| 13 |
|
| “Ku yi shiru ku ba ni zarafi in yi magana. Duk abin da zai faru, ya faru. |
|
| 14 |
|
| A shirye nake in yi kasai da raina. |
|
| 15 |
|
| Na fid da zuciya ɗungum. To, in Allah ya kashe ni, sai me? Zan faɗa masa ƙarata. |
|
| 16 |
|
| Mai yiwuwa ne ƙarfin halina ya cece ni, Tun da yake ba wani mugun mutumin da zai iya zuwa gaban Allah. |
|
| 17 |
|
| Sai a saurari bayanin da zan yi. |
|
| 18 |
|
| A shirye nake in faɗi ƙarata, Domin na sani ina da gaskiya. |
|
| 19 |
|
| “Ya Allah, za ka yi ƙarata? Idan kuwa ka yi, to, a shirye nake in yi shiru in mutu. |
|
| 20 |
|
| Ina da abu biyu da zan yi maka roƙo, Ka yarda da su, sa'an nan ba zan yi ƙoƙari in ɓoye ba. |
|
| 21 |
|
| Wato ka daina hukuncin da kake yi mini, Kada ka sa razanarka ta ragargaza ni. |
|
| 22 |
|
| “Ka fara yin magana, ya Allah, ni kuwa zan amsa. Ko kuma ka bari in yi magana, sa'an nan ka amsa mini. |
|
| 23 |
|
| Kuskure da laifi guda nawa na yi? Waɗanne irin laifofi ake tuhumata da su? |
|
| 24 |
|
| Me ya sa kake guduna? Me ya sa ka maishe ni kamar maƙiyi? |
|
| 25 |
|
| Ƙoƙari kake ka firgita ni? Ni ba wani abu ba ne, ganye ne kawai, Ka fāɗa wa tattaka da yaƙi ne kawai. |
|
| 26 |
|
| Ka kawo mugayen ƙararraki a kaina, Har da laifofin da na yi na ƙuruciya. |
|
| 27 |
|
| Ka ɗaure ƙafata da sarƙoƙi, Kakan lura da kowace takawata, Har kana bin diddigin sawayena. |
|
| 28 |
|
| Saboda wannan na zama abin kallo, ni kuwa kamar ragargazajjen itace ne, ko diddigaggiyar riga.” |
|
|
|
|