|
| 1 |
|
| “Idanuna sun ga waɗannan duka, kunnuwana sun ji sun kuma gane. |
|
| 2 |
|
| Abin da kuka sani, ni ma na sani; ba ku fi ni ba. |
|
| 3 |
|
| Amma ina so in yi magana da Maɗaukaki, in kai kukana wurin Allah kai tsaye. |
|
| 4 |
|
| Ku kuma kun ishe ni da ƙarairayi; ku likitocin wofi ne, dukanku! |
|
| 5 |
|
| In da za ku yi shiru gaba ɗaya! Zai zama muku hikima. |
|
| 6 |
|
| Ku ji gardamata yanzu; ku ji roƙon da zai fito daga bakina. |
|
| 7 |
|
| Za ku iya yin muguwar magana a madadin Allah? Ko za ku yi ƙarya a madadinsa? |
|
| 8 |
|
| Ko za ku nuna masa sonkai? Ko za ku yi gardama a madadinsa? |
|
| 9 |
|
| In ya bincike ku zai tarar ba ku da laifi? Ko za ku iya ruɗe shi yadda za ku ruɗi mutane? |
|
| 10 |
|
| Ba shakka zai kwaɓe ku in kun nuna sonkai a ɓoye. |
|
| 11 |
|
| Ko ikonsa ba ya ba ku tsoro? Tsoronsa ba zai auka muku ba? |
|
| 12 |
|
| Duk surutanku kamar toka suke; kāriyarku na yimɓu ne. |
|
| 13 |
|
| “Ku yi shiru zan yi magana; sa’an nan abin da zai same ni yă same ni. |
|
| 14 |
|
| Don me na sa kaina cikin hatsari na yi kasada da raina? |
|
| 15 |
|
| Ko da zai kashe ni ne, begena a cikinsa zai kasance; ba shakka zan kāre kaina a gabansa |
|
| 16 |
|
| lalle wannan zai kawo mini kuɓuta gama ba wani marar tsoron Allah da zai iya zuwa wurinsa! |
|
| 17 |
|
| Ku saurara da kyau ku ji abin da zan faɗa; bari kunnuwanku su ji abin da zan ce. |
|
| 18 |
|
| Yanzu da na shirya ƙarata, na san za a ce ba ni da laifi. |
|
| 19 |
|
| Ko wani zai ce ga laifin da na yi? In an same ni da laifi, zan yi shiru in mutu. |
|
| 20 |
|
| “Kai dai biya mini waɗannan bukatu biyu kawai ya Allah, ba zan kuwa ɓoye daga gare ka ba; |
|
| 21 |
|
| Ka janye hannunka nesa da ni, ka daina ba ni tsoro da bantsoronka. |
|
| 22 |
|
| Sa’an nan ka kira ni, zan kuwa amsa, ko kuma ka bar ni in yi magana sai ka amsa mini. |
|
| 23 |
|
| Abubuwa nawa na yi waɗanda ba daidai ba, kuma zunubi ne? Ka nuna mini laifina da zunubina. |
|
| 24 |
|
| Don me ka ɓoye mini fuskarka; ka kuma sa na zama kamar maƙiyinka? |
|
| 25 |
|
| Ko za a wahalar da ganye wanda iska take hurawa? Ko za ka bi busasshiyar ciyawa? |
|
| 26 |
|
| Gama ka rubuta abubuwa marasa daɗi game da ni; ka sa na yi gādon zunuban ƙuruciyata. |
|
| 27 |
|
| Ka daure ƙafafuna da sarƙa; kana kallon duk inda na taka ta wurin sa shaida a tafin ƙafafuna. |
|
| 28 |
|
| “Haka mutum yake lalacewa kamar ruɓaɓɓen abu, kamar rigar da asu ya cinye. |
|
|
|
|