|
| 1 |
|
| Sai Ayuba ya amsa, |
|
| 2 |
|
| “Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan; dukanku ba ku iya ta’aziyya ba! |
|
| 3 |
|
| Dogayen surutanku ba sa ƙare ne? Me yake sa kuke ta yin waɗannan surutai har kuke cin gaba da yin gardama? |
|
| 4 |
|
| Ni ma zan iya yin maganganu kamar yadda kuke yi in da kuna cikin halin da nake; zan iya faɗar duk abubuwan da kuke faɗi, in kaɗa muku kaina. |
|
| 5 |
|
| Amma bakina zai ƙarfafa ku; ta’aziyyar da za tă fito daga bakina za tă kawar muku da ɓacin zuciyarku. |
|
| 6 |
|
| “Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi; in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya. |
|
| 7 |
|
| Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni; ka ɓata gidana gaba ɗaya. |
|
| 8 |
|
| Ka daure ni, ya kuma zama shaida; yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa. |
|
| 9 |
|
| Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa yana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni; ya zura mini ido. |
|
| 10 |
|
| Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni; suka yi mini ba’a suka haɗu suka tayar mini. |
|
| 11 |
|
| Allah ya bashe ni ga mugayen mutane, ya jefa ni hannun mugaye. |
|
| 12 |
|
| Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai; amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya; ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi; |
|
| 13 |
|
| maharbansa sun kewaye ni. Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata har jini ya zuba a ƙasa. |
|
| 14 |
|
| Ya ji mini rauni a kai a kai ya auko mini kamar mai yaƙi. |
|
| 15 |
|
| “Ina makoki saye da tsummoki na ɓoye fuskata a cikin ƙura. |
|
| 16 |
|
| Fuskata ta yi ja don kuka idanuna sun kukumbura; |
|
| 17 |
|
| duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna ba kuma addu’ata mai tsabta ce. |
|
| 18 |
|
| “Ya duniya, kada ki ɓoye jinina; bari yă yi kuka a madadina! |
|
| 19 |
|
| Ko yanzu haka shaidata tana sama; wanda zai tsaya mini yana sama. |
|
| 20 |
|
| Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne yayinda nake kuka ga Allah; |
|
| 21 |
|
| a madadin mutum ya yi roƙo ga Allah kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa. |
|
| 22 |
|
| “Shekaru kaɗan suka rage in kama hanyar da ba a komawa. |
|
|
|
|