|
| 1 |
|
| Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa, |
|
| 2 |
|
| “Yaushe za ka gama maganganun nan? Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana. |
|
| 3 |
|
| Don me muke kamar shanu a wurinka, ka ɗauke mu mutanen wofi? |
|
| 4 |
|
| Kai da ka yayyage kanka don haushi, za a yashe duniya saboda kai ne? Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu? |
|
| 5 |
|
| “An kashe fitilar mugu; harshen wutarsa ya daina ci. |
|
| 6 |
|
| Wutar cikin tentinsa ta zama duhu; fitilar da take kusa da shi ta mutu. |
|
| 7 |
|
| Ƙarfin takawarsa ya ragu; dabararsa ta ja fāɗuwarsa. |
|
| 8 |
|
| Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga, yana ta yawo a cikin ragar. |
|
| 9 |
|
| Tarko ya kama ɗiɗɗigensa; tarko ya riƙe shi kam. |
|
| 10 |
|
| An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa; an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi. |
|
| 11 |
|
| Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefe yana bin shi duk inda ya je. |
|
| 12 |
|
| Masifa tana jiransa; bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi. |
|
| 13 |
|
| Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa; ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa. |
|
| 14 |
|
| An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsa aka sa shi tsoro sosai. |
|
| 15 |
|
| Wuta ta cinye tentinsa; farar wuta ta rufe wurin da yake zama. |
|
| 16 |
|
| Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasa rassansa sun mutu a sama. |
|
| 17 |
|
| An manta da shi a duniya; ba wanda yake ƙara tunawa da shi. |
|
| 18 |
|
| An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu, an kore shi daga duniya. |
|
| 19 |
|
| Ba shi da ’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa, ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama. |
|
| 20 |
|
| Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi; tsoro ya kama mutanen gabas. |
|
| 21 |
|
| Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake, haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.” |
|
|
: |
| 1 | | 2 | | 3 | | 4 | | 5 | | 6 | | 7 | | 8 | | 9 | | 10 | | 11 | | 12 | | 13 | | 14 | | 15 | | 16 | | 17 | | 18 | | 19 | | 20 | | 21 | 1
1
1 |
|
|---|
|
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/job/018.mp3
42
18