|
| 1 |
|
| Ayuba ya amsa. |
|
| 2 |
|
| “Me ya sa kuke azabta ni da maganganu? |
|
| 3 |
|
| A kowane lokaci kuna wulakanta ni, Ba kwa jin kunya yadda kuke zagina. |
|
| 4 |
|
| Da a ce ma na aikata abin da yake ba daidai ba ne, Da me ya cuce ku? |
|
| 5 |
|
| Tsammani kuke kun fi ni ne, Kuna ɗauka cewa wahalar da nake sha Ta tabbatar ni mai laifi ne. |
|
| 6 |
|
| Ba ku iya ganin abin da Allah ya yi mini, Ya kafa tarko don ya kama ni. |
|
| 7 |
|
| Na ce ban yarda da kama-karyarsa ba, Amma ba wanda ya kasa kunne. Na nema a aikata gaskiya, amma sam, babu. |
|
| 8 |
|
| Allah ya rufe hanya, na kasa wucewa, Ya rufe hanyata da duhu, |
|
| 9 |
|
| Gama ya kwashe dukiyata duka, Ya ɓata mini suna. |
|
| 10 |
|
| Ya mammangare ni, Ya tumɓuke sa zuciyata, Ya bar ni in yi yaushi, in mutu. |
|
| 11 |
|
| Allah ya zaburo mini da fushi, Ya maishe ni kamar mafi mugunta daga cikin maƙiyansa. |
|
| 12 |
|
| Ya aiko da rundunar sojansa don ta fāɗa mini, Suka haƙa ramummuka kewaye da alfarwata inda za su yi kwanto. |
|
| 13 |
|
| “'Yan'uwana sun yashe ni, Na zama baƙo ga idon sanina. |
|
| 14 |
|
| Dangina da abokaina sun tafi. |
|
| 15 |
|
| Waɗanda sukan ziyarce gidana sun manta da ni. Barorina mata na gidana sun maishe ni kamar baƙo daga wata ƙasa. |
|
| 16 |
|
| Sa'ad da na kira barana, ba ya amsawa, Ko a lokacin da na roƙe shi ya taimake ni. |
|
| 17 |
|
| Har matata ma ba ta iya jurewa da ɗoyin numfashina, 'Yan'uwana maza kuwa ba su ko zuwa kusa da ni. |
|
| 18 |
|
| 'Yan yara sukan raina ni su yi mini dariya sa'ad da suka gan ni. |
|
| 19 |
|
| Aminaina na kusa sukan dube ni, duban ƙyama, Waɗanda na fi ƙaunarsu duka sun zama maƙiyana. |
|
| 20 |
|
| Fatar jikina ta saki, ba ƙarfi, Da ƙyar na kuɓuta. |
|
| 21 |
|
| Ku abokaina ne! Ku ji tausayina! Ikon Allah ya fyaɗa ni ƙasa. |
|
| 22 |
|
| Me ya sa kuke ɓata mini rai kamar yadda Allah ya yi? Azabar da kuka yi mini har yanzu ba ta isa ba? |
|
| 23 |
|
| “Da ma a ce wani zai rubuta abin da nake faɗa, Ya rubuta shi a littafi! |
|
| 24 |
|
| Ko kuwa ya zana kalmomina da kurfi a kan dutse, Ya rubuta su don su tabbata har abada! |
|
| 25 |
|
| Amma na sani akwai wani a Samaniya Wanda a ƙarshe zai zo ya tsaya mini. |
|
| 26 |
|
| Ko da yake ciwo ya riga ya cinye fatata, A wannan jiki zan ga Allah. |
|
| 27 |
|
| Zan gan shi ido da ido, Ba kuwa zai zama baƙo a gare ni ba. “Zuciyata ta karai saboda ku mutane kun ce, |
|
| 28 |
|
| ‘Ta ƙaƙa za mu yi masa azaba?’ Kuna neman sanadin da za ku fāɗa mini. |
|
| 29 |
|
| Amma yanzu, sai ku ji tsoron takobi, Ku ji tsoron takobin da yake kawo hasalar Allah a kan zunubi. Don haka za ku sani akwai wani mai yin shari'a.” |
|
|
|
|