|
| 1 |
|
| Sai Ayuba ya amsa, |
|
| 2 |
|
| “Har yaushe za ku yi ta ba ni azaba ku kuma murƙushe ni da maganganunku? |
|
| 3 |
|
| Yanzu sau goma ke nan kuna wulaƙanta ni, kuna kai mini hari na rashin kunya. |
|
| 4 |
|
| In gaskiya ne na yi laifi, kuskurena ya rage nawa. |
|
| 5 |
|
| In kuwa za ku ɗaukaka kanku a kaina kuna ɗauka wahalar da nake sha domin na yi laifi ne, |
|
| 6 |
|
| sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba ya kewaye ni da ragarsa. |
|
| 7 |
|
| “Ko da yake na yi kuka cewa, ‘An yi mini ba daidai ba!’ Ba a amsa mini ba; ko da yake na nemi taimako, ba a yi adalci ba. |
|
| 8 |
|
| Ya tare mini hanya yadda ba zan iya wucewa ba; ya rufe hanyata da duhu. |
|
| 9 |
|
| Ya cire darajar da nake da ita, ya kuma cire rawani daga kaina. |
|
| 10 |
|
| Ya yi kaca-kaca da ni har sai da na ƙare; ya tuge begen da nake da shi kamar itace. |
|
| 11 |
|
| Yana jin haushina ya lissafta ni cikin maƙiyansa. |
|
| 12 |
|
| Rundunarsa ta zo da ƙarfi; suka kafa sansani kewaye da ni, suka zagaye tentina. |
|
| 13 |
|
| “Ya raba ni da ’yan’uwana maza; abokaina sun zama baƙi gare ni. |
|
| 14 |
|
| Dangina sun tafi; abokaina na kurkusa sun manta da ni. |
|
| 15 |
|
| Waɗanda sukan ziyarce ni, da masu yi mini aiki mata sun ɗauke ni baƙo. |
|
| 16 |
|
| Na kira bawana, amma bai amsa ba, ko da yake na roƙe shi da bakina. |
|
| 17 |
|
| Numfashina yana ɓata wa matata rai; ’yan’uwana sun ƙi ni. |
|
| 18 |
|
| Har ’yan yara suna rena ni; in sun gan ni sai su fara yi mini riyar reni. |
|
| 19 |
|
| Duk abokaina sun yashe ni; waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata. |
|
| 20 |
|
| Ni ba kome ba ne sai dai fata da ƙashi, da ƙyar na tsira. |
|
| 21 |
|
| “Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina, gama hannun Allah ya sauko a kaina. |
|
| 22 |
|
| Don me kuke fafarata kamar yadda Allah yake yi? Ba ku gaji da yagar fatata ba? |
|
| 23 |
|
| “Kash, da ma a ce ana rubuta maganganuna, da an rubuta su a littafi, |
|
| 24 |
|
| a rubuta su da ƙarfe a kan dutse don su dawwama har abada! |
|
| 25 |
|
| Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya. |
|
| 26 |
|
| Kuma bayan an hallaka fatata, duk da haka a cikin jiki zan ga Allah. |
|
| 27 |
|
| Zan gan shi da kaina da idanuna, Ni, ba wani ba ne. Zuciyata ta cika da wannan tunani! |
|
| 28 |
|
| “In kuka ce, ‘Za ku ci gaba da matsa mini, tun da shi ne tushen damuwa,’ |
|
| 29 |
|
| sai ku ma ku ji tsoron takobin; gama fushi yakan kawo hukunci ta wurin takobi, sa’an nan za ku san cewa akwai shari’a.” |
|
|
: |
| 1 | | 2 | | 3 | | 4 | | 5 | | 6 | | 7 | | 8 | | 9 | | 10 | | 11 | | 12 | | 13 | | 14 | | 15 | | 16 | | 17 | | 18 | | 19 | | 20 | | 21 | | 22 | | 23 | | 24 | | 25 | | 26 | | 27 | | 28 | | 29 | 1
1
1 |
|
|---|
|
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/job/019.mp3
42
19