|
| 1 |
|
| Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa, |
|
| 2 |
|
| “Mutum yana iya zama da amfani a wurin Allah? Mai hikima ma zai iya zama da amfani a wurin shi? |
|
| 3 |
|
| Wane daɗi Allah zai ji in kai mai adalci ne? Wace riba zai samu in rayuwarka marar laifi ce? |
|
| 4 |
|
| “Ko don kana tsoron Allah shi ya sa ya kwaɓe ka ya kuma bari haka yă same ka? |
|
| 5 |
|
| Ba muguntarka ce ta yi yawa ba? Ba zunubanka ne ba iyaka ba? |
|
| 6 |
|
| Ka sa ɗan’uwanka yă biya ka bashin da kake binsa ba dalili; ka ƙwace wa mutanen rigunansu ka bar su tsirara. |
|
| 7 |
|
| Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci. |
|
| 8 |
|
| Ko da yake kai mai ƙarfi ne, ka mallaki ƙasa, mutum mai martaba kuma, kana zama cikin ƙasarka. |
|
| 9 |
|
| Ka kori gwauraye hannu wofi, ka kuma karya ƙarfin marayu. |
|
| 10 |
|
| Shi ya sa kake kewaye da tarkuna, shi ya sa ka cika da tsoron mugun abin da zai auko maka. |
|
| 11 |
|
| An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani, shi ya sa ambaliyar ruwa ta rufe ka. |
|
| 12 |
|
| “Ba Allah ne a can sama ba? Dubi yadda taurarin sama suke can nesa a sama! |
|
| 13 |
|
| Duk da haka ka ce, ‘Me Allah ya sani? A cikin duhu ne yake shari’a? |
|
| 14 |
|
| Gajimare ya rufe shi, saboda haka ba ya ganinmu lokacin da yake takawa a cikin sammai.’ |
|
| 15 |
|
| Za ka ci gaba da bin tsohuwar hanyar da mugayen mutane suka bi? |
|
| 16 |
|
| An ɗauke su kafin lokacinsu yă cika, ruwa ya share tushensu. |
|
| 17 |
|
| Suka ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu! Me Maɗaukaki zai yi mana?’ |
|
| 18 |
|
| Duk da haka kuwa shi ne ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau, saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye. |
|
| 19 |
|
| “Masu adalci suna gani ana hallaka mugaye, suna jin daɗi; marasa laifi suna yi musu ba’a, suna cewa, |
|
| 20 |
|
| ‘Ba shakka an hallaka maƙiyanmu, wuta kuma ta ƙona dukiyarsu.’ |
|
| 21 |
|
| “Ka miƙa kanka ga Allah ka samu salamarsa; ta haka ne arziki zai zo maka. |
|
| 22 |
|
| Ka bi umarnin da zai fito daga bakinsa kuma ka riƙe maganarsa a cikin zuciyarka. |
|
| 23 |
|
| In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke. In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka. |
|
| 24 |
|
| Ka jefar da zinariyarka a ƙasa, ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu, |
|
| 25 |
|
| sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka, zai zama azurfa mafi kyau a wurinka. |
|
| 26 |
|
| Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki daga wurin Maɗaukaki, ku kuma ɗaga idanunku ga Allah |
|
| 27 |
|
| Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka, kuma za ka cika alkawuranka. |
|
| 28 |
|
| Abin da ka zaɓa za ka yi za ka yi nasara a ciki, haske kuma zai haskaka hanyarka. |
|
| 29 |
|
| Sa’ad da aka ƙasƙantar da mutane ka kuma ce, ‘A ɗaga su!’ Sa’an nan zai ceci masu tawali’u. |
|
| 30 |
|
| Zai ceci wanda ma yake mai laifi, wanda zai tsirar da shi ta wurin tsabtar hannuwanka.” |
|
|
|
|