Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ayuba ya amsa. |
| 2 |
| “Duk da haka zan yi tawaye in yi wa Allah gunaguni, In dinga yin nishi. |
| 3 |
| Da ma na san inda zan same shi, In kuma san yadda zan kai wurinsa, |
| 4 |
| Da zan kai ƙarata a gare shi, in faɗa masa duk muhawarata, in kāre kaina ne. |
| 5 |
| Ina so in san irin amsar da zai mayar mini, Ina kuma so in san yadda zai amsa mini. |
| 6 |
| Allah kuwa da dukan ƙarfinsa zai yi gāba da ni? A'a, zai saurara in na yi magana. |
| 7 |
| Ina da aminci, zan faɗa wa Allah ra'ayina, Zai tabbatar da amincina duka. |
| 8 |
| “Na nemi Allah a gaba, amma ban same shi a can ba, Ban kuwa same shi a baya ba sa'ad da na neme shi. |
| 9 |
| Allah ya tafi wurin aiki a dama, Ya kuma tafi hagu, amma har yanzu ban gan shi ba. |
| 10 |
| Duk da haka Allah ya san kowane irin hali da nake ciki. Idan ya jarraba ni zai tarar ni tsattsarka ne. |
| 11 |
| Da aminci ina bin hanyar da ya zaɓa, Ban kuwa taɓa kaucewa daga wannan gefe zuwa wancan ba. |
| 12 |
| A kullum ina aikata abin da Allah ya umarta, Ina bin nufinsa, ba nufin kaina ba. |
| 13 |
| “Bai taɓa sākewa ba. Ba wanda zai iya gāba da shi, Ko kuma ya hana shi yin abin da yake so ya aikata. |
| 14 |
| Zai tabbatar da abin da ya shirya domina, Wannan ma ɗaya daga cikin shirye-shiryen da ya yi ne. |
| 15 |
| Don haka in rawar jiki a gabansa saboda tsoro. |
| 16 |
| Allah Mai Iko Dukka ya lalatar da ƙarfin halina. Allah ne ya tsorata ni, |
| 17 |
| Amma ban damu da damu ba, Ko da yake duhu ya dunɗe idanuna.” |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/job/023.mp3
42
23