Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Sa’an nan Ayuba ya amsa, |
| 2 |
| “Ko a yau, ina kuka mai zafi; hannunsa yana da nauyi duk da nishin da nake yi. |
| 3 |
| Da a ce na san inda zan same shi; da a ce zan iya zuwa wurin da yake zama! |
| 4 |
| Zan kai damuwata wurinsa in yi gardama da shi. |
| 5 |
| Zan nemi in san abin da zai ce mini, in kuma auna abin da zai ce mini. |
| 6 |
| Zai yi gardama da ni da ikonsa mai girma? Babu, ba zai zarge ni da laifi ba. |
| 7 |
| Mai adalci ne zai kawo ƙara a wurinsa, kuma zan samu kuɓuta daga wurin mai shari’an nan har abada. |
| 8 |
| “Amma in na je gabas, ba ya wurin; in na je yamma, ba zan same shi ba. |
| 9 |
| Sa’ad da yake aiki a arewa, ba ni ganinsa; sa’ad da ya juya zuwa kudu, ba na ganinsa. |
| 10 |
| Amma ya san hanyar da nake bi; sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya. |
| 11 |
| Ƙafafuna suna bin ƙafafunsa kurkusa; na bi hanyarsa ba tare da na juya ba. |
| 12 |
| Ban fasa bin dokokin da ya bayar ba; na riƙe maganarsa da muhimmanci fiye da abincin yau da gobe. |
| 13 |
| “Amma ya tsaya shi kaɗai, kuma wa ya isa yă ja da shi? Yana yin abin da yake so. |
| 14 |
| Yana yi mini abin da ya shirya yă yi mini, kuma yana da sauran irinsu a ajiye. |
| 15 |
| Shi ya sa na tsorata a gabansa; sa’ad da na yi tunanin wannan duka, nakan ji tsoronsa. |
| 16 |
| Allah ya sa zuciyata ta yi sanyi; Maɗaukaki ya tsorata ni. |
| 17 |
| Duk da haka duhun bai sa in yi shiru ba, duhun da ya rufe mini fuska. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/job/023.mp3
42
23