|
| 1 |
|
| “Domin me Maɗaukaki ba zai sa ranar shari’a ba? Don me waɗanda suka san shi suke faman samun irin ranakun nan? |
|
| 2 |
|
| Mugaye suna satar fili ta wurin matsar da duwatsun da aka yi iyaka da su; suna satar dabbobi su kuma yi kiwon su. |
|
| 3 |
|
| Suna ƙwace wa marayu jakunansu suna kuma ƙwace wa gwauruwa sa don suna binta bashi. |
|
| 4 |
|
| Suna ture matalauta daga hanya suna kuma sa dole matalautan ƙasar su ɓoye. |
|
| 5 |
|
| Kamar jakunan jeji a hamada, matalauta suna aikin neman abinci gonaki marasa amfani suna tanada abinci wa ’ya’yansu. |
|
| 6 |
|
| Suna girbi a gonakin da ba nasu ba, suna yin kala a gonar inabi ta mugaye. |
|
| 7 |
|
| Don ba su da tufafi, sukan kwana tsirara; ba su da wani abin da zai rufe su cikin sanyi. |
|
| 8 |
|
| Sun jiƙe sharkaf da ruwan da yake kwararowa daga duwatsu, sun rungume duwatsu don rashin wurin fakewa. |
|
| 9 |
|
| Ana ƙwace jinjiri mai shan mama; ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi. |
|
| 10 |
|
| Don ba su da tufafi suna yawo tsirara; suna dakon dammunan hatsi amma duk da haka suna cikin shan yunwa. |
|
| 11 |
|
| Suna matse zaitun a cikin kunyoyi suna kuma matse ruwan inabi daga ’ya’yan inabi, duk da haka suna fama da ƙishi. |
|
| 12 |
|
| Ana jin nishin masu mutuwa daga birni, kuma rayukan waɗanda aka ji musu rauni suna kuka suna kira don taimako. Amma bai ba wani laifi ba. |
|
| 13 |
|
| “Akwai waɗanda suke yi wa haske tawaye, waɗanda ba su san hanyoyinsa ba ko kuma ba su taɓa bin hanyoyinsa ba. |
|
| 14 |
|
| Sa’ad da hasken yini ya tafi, mai kisankai yakan tashi; yă je yă kashe matalauta da masu bukata; a cikin dare yake shigowa kamar ɓarawo. |
|
| 15 |
|
| Idanun mazinaci suna jiran yamma ta yi sosai; yana tunani cewa, ‘Ba wanda zai gan ni,’ sai kuma yă ɓoye fuskarsa. |
|
| 16 |
|
| Cikin duhu mutane suna fasa gidaje, amma da rana sukan kulle kansu; ba sa so wani abu yă haɗa su da haske. |
|
| 17 |
|
| Gama dukansu, duhu mai yawa shi ne safiyarsu; suna abokantaka da razanar duhu. |
|
| 18 |
|
| “Duk da haka kamar abu marar nauyi suke a kan ruwa; gefen ƙasar da suke, an la’anta ta, yadda ba wanda yake zuwa gonar inabinsu. |
|
| 19 |
|
| Kamar yadda zafi da fări suke shanye ƙanƙarar da ta narke, haka kabari zai ƙwace waɗanda suka yi zunubi. |
|
| 20 |
|
| Waɗanda suka haife su za su manta da su, tsutsotsi za su cinye su; ba za a sāke tunawa da mugaye ba amma an sare su kamar itace. |
|
| 21 |
|
| Suna cutar macen da ba ta da ɗa, suna nuna wa gwauruwa rashin alheri. |
|
| 22 |
|
| Amma Allah cikin ikonsa yakan kawar da masu ƙarfi, ko da yake sun yi ƙarfi, ba su da tabbacin rayuwa. |
|
| 23 |
|
| Mai yiwuwa zai bar su su zauna cikin kwanciyar hankali, amma idanunsa suna kansu. |
|
| 24 |
|
| Sukan samu cin nasara na ɗan lokaci, amma kuma za su ɓace; za su fāɗi a tattara su kamar sauran; za a datse su kamar kan hatsi. |
|
| 25 |
|
| “In wannan ba haka ba ne, wane ne zai shaida ƙarya nake yi har yă ƙi yarda da maganata?” |
|
|
|
|