Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Ayuba ya amsa. |
| 2 |
| “Kai ne mai taimakon marar ƙarfi, Kai ne mai ceton rarrauna! |
| 3 |
| Kai ne kake ba marar hikima shawara, Kai kake sanar da ilimi mai ma'ana a wadace! |
| 4 |
| Kana tsammani wane ne zai ji maganganunka duka? Wane ne ya iza ka ka yi irin wannan magana? |
| 5 |
| “Lahira tana rawa, Mazaunanta suna rawar jiki don tsoro. |
| 6 |
| Lahira tsirara take a gaban Allah, Haka kuma Halaka take a gaban Allah. |
| 7 |
| Allah ne ya shimfiɗa arewa a sarari kurum, Ya rataya duniya ba bisa kan kome ba. |
| 8 |
| Allah ne ya cika gizagizai masu duhu da ruwa, Girgijen kuwa bai kece ba. |
| 9 |
| Ya rufe kursiyinsa, ya shimfiɗa girgije a kansa. |
| 10 |
| Ya shata da'ira a kan fuskar teku, A kan iyakar da take tsakanin haske da duhu. |
| 11 |
| Ginshiƙan samaniya sun girgiza, Sun firgita saboda tsautawarsa. |
| 12 |
| Ta wurin ƙarfinsa ya kwantar da teku, Da saninsa ya hallaka dodon ruwan nan, wato Rahab. |
| 13 |
| Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi garau, Ikonsa ne kuma ya sha zarar macijin nan mai gudu. |
| 14 |
| Amma waɗannan kaɗan ne kawai daga cikin al'amuransa. Ɗan ƙis kaɗai muke ji a kansa. Amma wa zai iya fahimtar ikon tsawarsa?” |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/job/026.mp3
42
26