Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Sai Ayuba ya amsa, |
| 2 |
| “Yadda ka taimaki marar ƙarfi! Yadda ka ceci marar ƙarfi! |
| 3 |
| Ka ba marar hikima shawara! Ka nuna kana da ilimi sosai. |
| 4 |
| Wane ne ya taimake ka ka yi waɗannan maganganu? Kuma ruhun wane ne ya yi magana ta bakinka? |
| 5 |
| “Matattu suna cikin azaba, waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye da dukan mazauna cikin ruwaye. |
| 6 |
| Mutuwa tsirara take a gaban Allah; haka kuma hallaka take a buɗe. |
| 7 |
| Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari; ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba. |
| 8 |
| Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa, duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba. |
| 9 |
| Ya rufe fuskar wata, ya shimfiɗa gizagizai a kan shi, |
| 10 |
| ya zāna iyakar fuskar ruwa a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske. |
| 11 |
| Madogaran sama sun girgiza, saboda tsawatawarsa. |
| 12 |
| Da ikonsa ya kwantar da teku; da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab. |
| 13 |
| Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu. |
| 14 |
| Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa. Kaɗan kawai muke ji game da shi! Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?” |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/job/026.mp3
42
26