Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ayuba kuwa ya ci gaba da magana, |
| 2 |
| “Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata, Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai. |
| 3 |
| Muddin ina da rai a cikina kuma numfashin Allah yana cikin hancina, |
| 4 |
| bakina ba zai faɗi mugun abu ba, harshena kuma ba zai yi ƙarya ba. |
| 5 |
| Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba; har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba. |
| 6 |
| Zan ci gaba da adalcina, ba zan fasa ba; lamirina ba zai taɓa yashe ni ba, dukan kwanakin raina. |
| 7 |
| “Bari maƙiyana su zama kamar mugaye, masu gāba da ni kuma su zama kamar marasa adalci. |
| 8 |
| Gama wane bege marar tsoron Allah yake da shi, lokacin da aka datse shi, lokacin da Allah ya ɗauke ransa? |
| 9 |
| Ko Allah yana sauraron kukansa lokacin da ƙunci ya auko masa? |
| 10 |
| Ko zai sami farin ciki daga Maɗaukaki? Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci? |
| 11 |
| “Zan koya muku game da ikon Allah; ba zan ɓoye hanyoyin Maɗaukaki ba. |
| 12 |
| Duk kun ga wannan ku da kanku saboda haka me ya sa kuke maganganun nan marasa ma’ana? |
| 13 |
| “Ga abin da mugaye za su samu gādon da azzalumi zai samu daga Maɗaukaki. |
| 14 |
| Kome yawan ’ya’yansa, takobi za tă gama da su; zuriyarsa ba za su taɓa samun isashen abinci ba. |
| 15 |
| Waɗanda suka tsira annoba za tă kashe su, kuma gwaurayensu ba za su yi kukan mutuwarsu ba. |
| 16 |
| Ko da yake ya tara azurfa kamar ƙasa, tufafi kuma kamar tarin ƙasa, |
| 17 |
| abin da ya tara masu adalci za su sa marasa laifi za su raba azurfarsa. |
| 18 |
| Gidan da ya gina kamar gidan gizo-gizo, kamar bukkar mai tsaro. |
| 19 |
| Attajiri zai kwanta, amma daga wannan shi ke nan; lokacin da zai buɗe idanunsa, kome ya tafi. |
| 20 |
| Tsoro zai kwashe shi kamar ambaliyar ruwa; Da dare iska za tă tafi da shi. |
| 21 |
| Iskar gabas za tă tafi da shi; shi ke nan ya ƙare; za tă share shi daga wurinsa. |
| 22 |
| Za tă murɗe shi ba tausayi, lokacin da yake guje wa ikon iskar. |
| 23 |
| Zai tafa hannu yă yi tsaki yă kawar da shi daga wurinsa.” |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/job/027.mp3
42
27