|
| 1 |
|
| Akwai ramin azurfa akwai kuma wurin da ake tace zinariya. |
|
| 2 |
|
| Daga cikin ƙasa ake ciro ƙarfe, ana kuma narkar da tagulla daga cikin dutse. |
|
| 3 |
|
| Mutum ya kawo ƙarshen duhu; yakan bincike zuzzurfar iyaka, yana neman duwatsu a wuri mafi duhu. |
|
| 4 |
|
| Nesa da inda mutane suke zama, yakan huda rami yă yi abin lilo, a wurin da mutane ba sa bi. |
|
| 5 |
|
| Cikin ƙasa inda ake samun abinci, a ƙarƙashinta kuwa zafi ne kamar wuta; |
|
| 6 |
|
| akwai duwatsu masu daraja a cikin duwatsunta, akwai kuma zinariya a cikin ƙurarta. |
|
| 7 |
|
| Tsuntsu mai farauta bai san hanyarta ba, ba shahon da ya taɓa ganin ta. |
|
| 8 |
|
| Manyan namun jeji ba su taɓa binta ba, ba zakin da ya taɓa binta. |
|
| 9 |
|
| Hannun mutum ya iya sarrafa ƙanƙarar duwatsu, yă kuma tumɓuke tushen duwatsu. |
|
| 10 |
|
| Yana tona rami a cikin duwatsu idanunsa suna ganin dukan dukiyar da ke cikin duwatsun. |
|
| 11 |
|
| Yana nema daga ina ruwan rafi yake ɓulɓulowa yana kuma binciko abubuwan da suke a ɓoye yă kawo su cikin haske. |
|
| 12 |
|
| Amma a ina ne za a iya samun hikima? Ina fahimta take zama? |
|
| 13 |
|
| Mutum bai gane muhimmancinta ba, ba a samunta a ƙasar masu rai. |
|
| 14 |
|
| Zurfi ya ce, “Ba ta wurina”; teku ya ce, “Ba ta wurina.” |
|
| 15 |
|
| Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta, ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa. |
|
| 16 |
|
| Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir, ko sauran duwatsu masu daraja ba. |
|
| 17 |
|
| Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba, ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba. |
|
| 18 |
|
| Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya; farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai. |
|
| 19 |
|
| Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba, zallar zinariya ma ba tă isa ta saye ta ba. |
|
| 20 |
|
| “To, daga ina ke nan hikima ta fito? Ina fahimta take zama? |
|
| 21 |
|
| An ɓoye ta daga idanun kowane abu mai rai, har tsuntsayen sararin sama ma an ɓoye masu ita. |
|
| 22 |
|
| Hallaka da mutuwa suna cewa, ‘Jita-jitarta kaɗai muke ji.’ |
|
| 23 |
|
| Allah ya gane hanyar zuwa wurinta. Shi ne kaɗai ya san inda take zama, |
|
| 24 |
|
| Gama yana ganin iyakar duniya kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama. |
|
| 25 |
|
| Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura, ya kuma auna ruwaye. |
|
| 26 |
|
| Lokacin da ya yi wa ruwan sama doka da kuma hanya domin walƙiya, |
|
| 27 |
|
| sai ya dubi hikima ya auna ta; ya tabbatar da ita, ya gwada ta. |
|
| 28 |
|
| Ya kuma ce wa mutum, ‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima, kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ” |
|
|
|
|