|
| 1 |
|
| Ayuba ya yi magana ya la'anci ranar da aka haife shi. |
|
| 2 |
|
| Ya ce, “Ya Ubangiji, ka la'anci ranan nan da aka haife ni. |
|
| 3 |
|
| Ka la'anci daren nan da aka yi cikina. |
|
| 4 |
|
| Ka mai da ranan nan ta zama duhu, ya Allah. Kada a ƙara tunawa da wannan rana, Kada haske ya ƙara haskakata. |
|
| 5 |
|
| Ka sa ta zama ranar duhu baƙi ƙirin. Ka rufe ta da gizagizai, kada hasken rana ya haskaka ta. |
|
| 6 |
|
| Ka shafe wannan dare daga cikin shekara, Kada kuma a ƙara lasafta shi. |
|
| 7 |
|
| Ka sa daren ya zama marar amfani, daren baƙin ciki. |
|
| 8 |
|
| Ka faɗa wa masu sihiri su la'anci wannan rana, Su waɗanda suke umartar dodon ruwa. |
|
| 9 |
|
| Ka hana gamzaki haskakawa, Kada ka bar daren nan ya sa zuciya ga wayewar gari, |
|
| 10 |
|
| Ka la'anci daren nan da aka haife ni, Da ya jefa ni a baƙin ciki da wahala. |
|
| 11 |
|
| “Da ma na mutu tun a cikin cikin uwata, Ko kuwa da haihuwata in mutu. |
|
| 12 |
|
| Me ma ya sa uwata ta rungume ni a ƙirjinta, Ta shayar da ni kuma da mamanta? |
|
| 13 |
|
| Da a ce na mutu a lokacin, da yanzu ina huce, |
|
| 14 |
|
| Da ina ta barcina kamar sarakuna da masu mulki Waɗanda suka sāke gina fādodi na dā, |
|
| 15 |
|
| Da ina ta sharar barcina kamar shugabanni Waɗanda suka cika gidajensu da zinariya da azurfa, |
|
| 16 |
|
| In yi ta sharar barci kamar jariran da aka haifa matattu. |
|
| 17 |
|
| Mugaye za su daina muguntarsu a kabari, Ma'aikatan da suka gaji da aiki su ma za su huta, |
|
| 18 |
|
| Har 'yan sarƙa ma za su ji daɗin salama, Su huta daga tsautawa da umarnai masu tsanani. |
|
| 19 |
|
| Kowa da kowa yana wurin, babba da ƙarami duk ɗaya ne, Bayi ma sun sami 'yanci. |
|
| 20 |
|
| “Me ya sa ake barin mutane su yi ta zama cikin damuwa? Me ya sa ake ba da haske ga waɗanda suke baƙin ciki? |
|
| 21 |
|
| Sun jira mutuwa, amma ta ƙi samuwa, Sun fi son kabari da kowace irin dukiya. |
|
| 22 |
|
| Ba su da farin ciki, sai sun mutu an binne su tukuna. |
|
| 23 |
|
| Allah ya ɓoye musu sanin abin da zai faru nan gaba, Ya kalmashe su kowane gefe. |
|
| 24 |
|
| A maimakon cin abinci, sai baƙin ciki nake yi, Ba kuma zan daina yin nishi ba, |
|
| 25 |
|
| Dukan abin da nake jin tsoro ko fargaba ya faru. |
|
| 26 |
|
| Ba ni da salama, ba ni da hutawa, Wahala ba za ta taɓa ƙarewa ba.” |
|
|
|
|