|
| 1 |
|
| Bayan wannan Ayuba ya buɗe baki ya la’anta ranar da aka haife shi. |
|
| 2 |
|
| Ayuba ya ce, |
|
| 3 |
|
| “A hallaka ranar da aka haife ni, da kuma daren da aka ce, ‘An haifi jariri namiji!’ |
|
| 4 |
|
| Bari ranan nan ta zama duhu; kada Allah yă kula da ita; kada rana tă yi haske a wannan rana. |
|
| 5 |
|
| Bari duhu da inuwa mai duhu ta sāke rufe ta; gizagizai kuma su rufe ta; duhu kuma ya rufe haskenta. |
|
| 6 |
|
| Bari duhu mai yawa yă rufe daren nan; kada a haɗa ta cikin kwanakin shekara, ko kuma cikin kwanakin watanni. |
|
| 7 |
|
| Bari daren yă zama marar amfani; kada a ji wata sowa ta farin ciki. |
|
| 8 |
|
| Bari waɗanda suke la’anta ranaku su la’anta wannan rana su waɗanda suke umartar dodon ruwa. |
|
| 9 |
|
| Bari taurarinta na safe su zama duhu; bari ranar tă yi ta jiran ganin haske amma kada tă gani, |
|
| 10 |
|
| gama ba tă hana uwata ɗaukar cikina, don ta hana ni shan wahalan nan ba. |
|
| 11 |
|
| “Me ya sa ban mutu ba da za a haife ni, ko kuma in mutu sa’ad da ana haihuwata ba? |
|
| 12 |
|
| Me ya sa aka haife ni, aka tanada nono na sha na rayu? |
|
| 13 |
|
| Da yanzu ina kwance cikin salama; da ina barcina cikin salama |
|
| 14 |
|
| tare da sarakuna da mashawarta a cikin ƙasa, waɗanda suka gina wa kansu wuraren da yanzu duk sun rushe, |
|
| 15 |
|
| da shugabanni waɗanda suke da zinariya, waɗanda suka cika gidajensu da azurfa. |
|
| 16 |
|
| Ko kuma don me ba a ɓoye ni a cikin ƙasa kamar jaririn da aka haifa ba rai ba, kamar jaririn da bai taɓa ganin hasken rana ba. |
|
| 17 |
|
| A wurin mugaye za su daina yin mugunta, gajiyayyu kuma za su huta. |
|
| 18 |
|
| Waɗanda aka daure za su sami jin daɗin; an sake su ba za su sāke jin ana tsawata masu ba. |
|
| 19 |
|
| Manyan da ƙanana suna a can, bawa kuma ya sami ’yanci daga wurin maigidansa. |
|
| 20 |
|
| “Don me ake ba da haske ga waɗanda suke cikin ƙunci, rai kuma ga masu ɗacin rai |
|
| 21 |
|
| ga waɗanda suke neman mutuwa amma ba su samu ba, waɗanda suke nemanta kamar wani abu mai daraja a ɓoye, |
|
| 22 |
|
| waɗanda suke farin ciki sa’ad da suka kai kabari? |
|
| 23 |
|
| Don me aka ba mutum rai, mutumin da bai san wani abu game da kansa ba, mutumin da Allah ya kange shi. |
|
| 24 |
|
| Baƙin ciki ya ishe ni maimakon abinci; ina ta yin nishi ba fasawa; |
|
| 25 |
|
| Abin da nake tsoro ya faru da ni; abin da ba na so ya same ni. |
|
| 26 |
|
| Ba ni da salama, ba natsuwa; ba ni da hutu, sai wahala kawai.” |
|
|
|
|