|
| 1 |
|
| “Amma yanzu suna yi mini ba’a waɗanda na girme su, waɗanda iyayensu maza ba su isa su zama karnukan kiwon garken tumakina ba. |
|
| 2 |
|
| Ina amfani ƙarfin hannuwansu gare ni, tun da ba su da sauran kuzari? |
|
| 3 |
|
| Duk sun rame don rashi da yunwa, suna yawo a gaigayar ƙasa a kufai da dare. |
|
| 4 |
|
| A cikin jeji suna tsinkar ganyaye marasa daɗi, jijiyoyin itacen kwakwa ne abincinsu. |
|
| 5 |
|
| An kore su daga cikin mutanensu, aka yi musu ihu kamar ɓarayi. |
|
| 6 |
|
| An sa dole su zauna a kwazazzabai da kuma cikin kogunan duwatsu da kuma cikin ramummuka cikin ƙasa. |
|
| 7 |
|
| Suka yi ta kuka kamar dabbobi a jeji, suka taru a ƙarƙashin sarƙaƙƙiya. |
|
| 8 |
|
| Mutane marasa hankali marasa suna, an kore su daga ƙasar. |
|
| 9 |
|
| “Yanzu kuma ’ya’yansu maza su suke yi mini ba’a cikin waƙa na zama abin banza a gare su. |
|
| 10 |
|
| Suna ƙyamata suna guduna; suna tofa mini miyau a fuska. |
|
| 11 |
|
| Yanzu da Allah ya kunce bakana ya ba ni wahala sun raba ni da mutuncina. |
|
| 12 |
|
| A hannun damana ’yan tā-da-na-zaune-tsaye sun tayar; sun sa tarko a ƙafafuna, sun yi shirin hallaka ni. |
|
| 13 |
|
| Sun ɓata mini hanyata; sun yi nasara cikin hallaka ni, ba tare da wani ya taimake su ba. |
|
| 14 |
|
| Suka nufo ni daga kowane gefe; suka auko mini da dukan ƙarfinsu. |
|
| 15 |
|
| Tsoro ya rufe ni; an kawar mini mutuncina kamar da iska, dukiyata ta watse kamar girgije. |
|
| 16 |
|
| “Yanzu raina yana ƙarewa; kwanakin wahala sun kama ni. |
|
| 17 |
|
| Dare ya huda ƙasusuwana; ina ta shan azaba ba hutawa. |
|
| 18 |
|
| A cikin girman ikonsa Allah ya zama kamar riga a jikina; ya shaƙe ni kamar wuyan rigata. |
|
| 19 |
|
| Ya jefa ni cikin laka, na zama ba kome ba sai ƙura da toka. |
|
| 20 |
|
| “Na yi kuka gare ka ya Allah, amma ba ka amsa mini ba. Na tashi tsaye, amma sai ka dube ni kawai. |
|
| 21 |
|
| Ka dube ni ba tausayi; Ka kai mini hari da ƙarfin hannunka. |
|
| 22 |
|
| Ka ɗaga ni sama ka ɗora ni a kan iska; ka jujjuya ni cikin hadari. |
|
| 23 |
|
| Na san za ka sauko da ni ga mutuwa zuwa wurin da kowane mai rai zai je. |
|
| 24 |
|
| “Ba shakka ba mai ɗora hannu a kan mutumin da yake cikin wahala. Lokacin da ya yi kukan neman taimako a cikin wahalarsa. |
|
| 25 |
|
| Ashe ban yi kuka domin waɗanda suke cikin damuwa ba? Ko zuciyata ba tă yi baƙin ciki domin matalauta ba? |
|
| 26 |
|
| Duk da haka sa’ad da nake begen abu mai kyau, mugun abu ne ya zo; Sa’ad da nake neman haske, sai duhu ya zo. |
|
| 27 |
|
| Zuciyata ba tă daina ƙuna ba; ina fuskantar kwanakin wahala. |
|
| 28 |
|
| Na yi baƙi ƙirin, amma ba rana ce ta ƙona ni ba. Na tsaya a cikin mutane, na kuma yi kuka don taimako. |
|
| 29 |
|
| Na zama ɗan’uwan diloli, na zama abokan mujiyoyi. |
|
| 30 |
|
| Fatar jikina ta yi baƙi tana ɓarewa; jikina yana ƙuna da zazzaɓi. |
|
| 31 |
|
| Garayata ta zama ta makoki, sarewata kuma ta zama ta kuka. |
|
|
|
|