|
| 1 |
|
| Sai mutanen nan uku suka daina amsa wa Ayuba, domin a ganinsa shi mai adalci ne. |
|
| 2 |
|
| Amma Elihu ɗan Barakel mutumin Buz na iyalin Ram, ya ji haushi da Ayuba don yă nuna shi ne mai gaskiya ba Allah ba. |
|
| 3 |
|
| Ya kuma ji haushin abokan nan guda uku, don sun kāsa amsa wa Ayuba ko da yake sun nuna Ayuba ne yake da laifi. |
|
| 4 |
|
| Elihu ya jira sai a wannan lokaci ne ya yi magana da Ayuba, don shi ne yaro a cikinsu duka. |
|
| 5 |
|
| Amma sa’ad da Elihu ya ga mutanen nan uku ba su da abin cewa, sai ya fusata. |
|
| 6 |
|
| Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce, “Ni ƙarami ne a shekaru, ku kuma kun girme ni; shi ya sa na ji tsoro na kāsa gaya muku abin da na sani. |
|
| 7 |
|
| Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana; ya kamata yawan shekaru su koyar da hikima.’ |
|
| 8 |
|
| Amma ruhun da yake cikin mutum, numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa. |
|
| 9 |
|
| Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba, ba masu yawan shekaru ne suke gane abin da yake daidai ba. |
|
| 10 |
|
| “Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni; ni ma zan gaya muku abin da na sani. |
|
| 11 |
|
| Na jira sa’ad da kuke magana, na ji muhawwararku lokacin da kuke neman abin da za ku faɗa, |
|
| 12 |
|
| na saurare ku da kyau. Amma ba waninku da ya nuna Ayuba yana da laifi; ba ko ɗayanku da ya amsa muhawwararsa. |
|
| 13 |
|
| Kada ku ce, ‘Mun sami hikima; Allah ne kaɗai yake da ikon yin nasara da shi ba mutum ba.’ |
|
| 14 |
|
| Amma ba da ni Ayuba ya yi gardama ba kuma ba zan amsa masa da irin amsarku ba. |
|
| 15 |
|
| “Mamaki ya kama su kuma ba su da abin cewa; kalmomi sun kāsa musu. |
|
| 16 |
|
| Dole ne in jira yanzu da suka yi shiru, yanzu da suke tsaye a wurin ba su da amsa. |
|
| 17 |
|
| Ni ma zan faɗi nawa; ni ma zan faɗi abin da na sani. |
|
| 18 |
|
| Gama ina cike da magana, kuma ruhun da yake cikina yana iza ni; |
|
| 19 |
|
| a ciki ina kamar ruwan inabi wanda aka rufe a cikin kwalaba, kamar sabuwar salkar ruwan inabi mai shirin fashewa. |
|
| 20 |
|
| Dole in yi magana in sami lafiya; dole in buɗe baki in ba da amsa. |
|
| 21 |
|
| Ba zan nuna wa wani sonkai ba, ko kuma in yi wa wani daɗin baki ba; |
|
| 22 |
|
| gama da a ce na iya daɗin baki, da wanda ya yi ni ya ɗauke ni daga nan tuntuni. |
|
|
|
|