|
| 1 |
|
| “Amma yanzu, Ayuba, ka saurari abin da zan ce; ka sa hankali ga kowane abin da zan faɗa. |
|
| 2 |
|
| Zan yi magana; kalmomina suna dab da fitowa daga bakina. |
|
| 3 |
|
| Abin da zan faɗa gaskiya ne daga cikin zuciyata; bakina zai faɗi gaskiyar abin da na sani. |
|
| 4 |
|
| Ruhun Allah ne ya yi ni; numfashin Maɗaukaki ya ba ni rai. |
|
| 5 |
|
| Ka amsa mini in za ka iya; ka yi shirin fuskanta ta. |
|
| 6 |
|
| Ni kamar ka nake a gaban Allah; ni ma daga ƙasa aka yi ni. |
|
| 7 |
|
| Kada ka ji tsorona, ba abin da zai fi ƙarfinka. |
|
| 8 |
|
| “Amma ka faɗa na ji, na ji daidai abin da ka faɗa, |
|
| 9 |
|
| ‘ni mai tsarki ne marar zunubi; ina da tsabta kuma ba ni da laifi. |
|
| 10 |
|
| Duk da haka Allah ya same ni da laifi; ya ɗauke ni maƙiyinsa, |
|
| 11 |
|
| ya daure ƙafafuna da sarƙa; yana tsaron duk inda na bi.’ |
|
| 12 |
|
| “Amma na gaya maka, a nan ba ka yi daidai ba, gama Allah ya fi mutum girma. |
|
| 13 |
|
| Don me ka yi masa gunaguni cewa ba ya amsa tambayoyin mutum? |
|
| 14 |
|
| Gama Allah yana magana, yanzu ga wannan hanya, yanzu kuma ga wata hanya ko da yake ba lalle mutum yă lura ba. |
|
| 15 |
|
| A cikin mafarki, cikin wahayi da dare, sa’ad da barci mai zurfi ya fāɗo a kan mutane lokacin da suke cikin barci kan gadajensu, |
|
| 16 |
|
| mai yiwuwa yă yi musu magana a cikin kunnuwansu yă razana su da gargaɗinsa, |
|
| 17 |
|
| don a juyar da su daga abin da yake yi da ba daidai ba a kuma hana su daga girman kai, |
|
| 18 |
|
| don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami, a kāre su daga hallaka ta wurin takobi. |
|
| 19 |
|
| “Ko kuma mutum yă sha horo ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa, |
|
| 20 |
|
| yadda zai ji ƙyamar abinci, har yă ƙi son abinci mafi daɗi. |
|
| 21 |
|
| Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito. |
|
| 22 |
|
| Ransa yana matsawa kusa da rami, ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa. |
|
| 23 |
|
| Duk da haka, in akwai mala’ika a gefensa kamar matsakanci, ɗaya daga cikin dubu, da zai gaya wa mutum abin da yake daidai gare shi, |
|
| 24 |
|
| yă yi masa alheri yă ce, ‘Kada ka bari yă fāɗa cikin rami, na samu fansa dominsa.’ |
|
| 25 |
|
| Sa’an nan fatar jikinsa za tă zama sabuwa kamar ta jariri; za tă zama kamar lokacin da yake matashi. |
|
| 26 |
|
| Ya yi addu’a ga Allah ya kuwa samu alheri a wurinsa, yana ganin fuskar Allah yana kuma yin sowa don murna; Allah ya mayar da shi ya zama mai adalci. |
|
| 27 |
|
| Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce, ‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai, amma ban samu abin da ya kamata in samu ba. |
|
| 28 |
|
| Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami, kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’ |
|
| 29 |
|
| “Allah ya yi wa mutum duk waɗannan, sau biyu, har ma sau uku. |
|
| 30 |
|
| Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami, don hasken rai ya haskaka a kansa. |
|
| 31 |
|
| “Ka sa hankali da kyau, Ayuba, ka saurare ni; ka yi shiru zan yi magana. |
|
| 32 |
|
| In kana da abin da za ka ce, ka amsa mini; yi magana, domin ina so in ’yantar da kai. |
|
| 33 |
|
| Amma in ba haka ba, sai ka saurare ni; yi shiru, zan kuma koya maka hikima.” |
|
|
|
|