|
| 1 |
|
| Sa’an nan Elihu ya ce, |
|
| 2 |
|
| “Ku ji maganata, ku masu hikima; ku saurare ni, ku masu ilimi. |
|
| 3 |
|
| Gama kunne yana rarrabe magana kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci. |
|
| 4 |
|
| Bari mu zaɓi abin da yake daidai, bari mu koyi abin da yake mai kyau tare. |
|
| 5 |
|
| “Ayuba ya ce, ‘Ba ni da laifi, amma Allah ya hana mini hakkina. |
|
| 6 |
|
| Ko da yake ina da gaskiya, an ɗauke ni maƙaryaci; ko da yake ba ni da laifi, kibiyoyinsa sun ji mini ciwo wanda ba ya warkewa.’ |
|
| 7 |
|
| Wane mutum ne kamar Ayuba, wanda yake shan ba’a kamar ruwa? |
|
| 8 |
|
| Yana abokantaka da masu aikata mugunta; yana cuɗanya da mugaye. |
|
| 9 |
|
| Gama ya ce, ‘Ba ribar da mutum zai samu lokacin da yake ƙoƙari yă faranta wa Allah zuciya.’ |
|
| 10 |
|
| “Saboda haka ku saurare ni, ku masu ganewa. Ko kaɗan Allah ba ya mugunta, Maɗaukaki ba ya kuskure. |
|
| 11 |
|
| Yana biyan mutum bisa ga abin da ya yi; yana kawo masa abin da ayyukansa suka jawo. |
|
| 12 |
|
| Ba zai yiwu Allah yă yi ba daidai ba, Maɗaukaki ba zai yi shari’a marar gaskiya ba. |
|
| 13 |
|
| Wane ne ya ba shi iko yă lura da duniya? Wane ne ya ba shi iko kan dukan duniya? |
|
| 14 |
|
| In nufinsa ne ya kuma janye ruhunsa da numfashinsa, |
|
| 15 |
|
| ’yan adam duka za su hallaka tare, mutum kuma zai koma ƙasa. |
|
| 16 |
|
| “In kana da ganewa sai ka saurari wannan; ka saurari abin da zan ce. |
|
| 17 |
|
| Maƙiyin gaskiya zai iya yin mulki? Za ka iya ba mai gaskiya, Maɗaukaki laifi? |
|
| 18 |
|
| Ba shi ne ya ce wa sarakuna, ‘Ba ku da amfani ba,’ ya ce wa manya ‘Ku mugaye ne,’ |
|
| 19 |
|
| wanda ba ya nuna sonkai ga ’ya’yan sarki kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta, gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa. |
|
| 20 |
|
| Suna mutuwa nan take, a cikin tsakiyar dare; an girgiza mutanen amma sun wuce; an taɓa manya amma ba da hannun mutum ba. |
|
| 21 |
|
| “Idanunsa suna kan al’amuran mutane; yana ganin tafiyarsu duka. |
|
| 22 |
|
| Babu wuri mai duhu, babu inuwa mai duhu, inda masu aikata mugunta za su ɓoye. |
|
| 23 |
|
| Allah ba ya bukata yă ci gaba da bincike mutane, har da za su zo gabansa don yă shari’anta su. |
|
| 24 |
|
| Ba tare da tambaya ba yana ragargaza masu iko, yă kuma sa waɗansu a wurinsu. |
|
| 25 |
|
| Gama yana sane da abubuwan da suke yi, yana hamɓarar da su da dare a kuma ragargaza su. |
|
| 26 |
|
| Yana ba su horo, don muguntarsu, inda kowa zai gan su, |
|
| 27 |
|
| domin sun juya daga binsa, kuma ba su kula da hanyoyinsa ba. |
|
| 28 |
|
| Sun sa kukan matalauta ya kai wurinsa yadda ya kai ga jin kukan masu bukata. |
|
| 29 |
|
| Amma in ya yi shiru, wa zai ba shi laifi? In ya ɓoye fuskarsa, wa zai gan shi? Duk da haka shi yake da iko kan mutum da al’umma duka, |
|
| 30 |
|
| yana hana wanda bai san Allah ba yă yi mulki, ya hana shi sa wa mutane tarko. |
|
| 31 |
|
| “A ce mutum ya ce wa Allah, ‘Na yi laifi, amma ba zan sāke saɓa wa wani ba. |
|
| 32 |
|
| Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba; in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’ |
|
| 33 |
|
| Ya kamata Allah yă yi maka bisa ga abin da ka ce ne, sa’ad da ka ƙi ka tuba? Dole kai ka zaɓa, ba ni ba; yanzu ka gaya mini abin da ka sani. |
|
| 34 |
|
| “Mutane masu ganewa za su ce, masu hikima waɗanda suka ji ni za su ce mini, |
|
| 35 |
|
| ‘Ayuba ya yi magana cikin rashin sani; maganganunsa na marar hikima ne.’ |
|
| 36 |
|
| Kash, da za a gwada Ayuba har ƙarshe, domin yana ba da amsa kamar mugun mutum. |
|
| 37 |
|
| Ya ƙara tawaye a kan zunubansa; ya tafa hannuwansa na reni a cikinmu ya kuma ƙara yawan maganganunsa ga Allah.” |
|
|
|
|