Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Elihu kuwa ya yi magana. |
| 2 |
| “Ayuba, ba daidai ba ne, ka ce, Ba ka yi laifi a gaban Allah ba, |
| 3 |
| Ka kuwa ce, ‘Wace riba na ci? Wane fifiko nake da shi fiye da idan na yi zunubi?’ |
| 4 |
| Zan ba ka amsa, kai da abokanka. |
| 5 |
| Ka duba sama, Ka dubi gizagizai waɗanda suke can sama da kai. |
| 6 |
| Idan ka yi zunubi, da me ka cuci Allah? Idan ka aikata laifofi da yawa, wace cuta ka yi masa? |
| 7 |
| Idan kai adali ne da me ka ƙara masa, Ko kuwa me ya samu daga gare ka? |
| 8 |
| Muguntarka ta shafi mutum ne kamarka, Haka kuma adalcinka ya shafi ɗan adam ne kawai. |
| 9 |
| “Saboda yawan zalunci, jama'a sukan yi kuka, Suka nemi taimako, saboda matsin masu ƙarfi. |
| 10 |
| Amma ba su juyo wurin Allah Mahaliccinsu ba, Wanda yakan sa a raira waƙa da dare, |
| 11 |
| Wanda yake koya mana fiye da namomin jeji da suke a duniya, Wanda ya sa muka fi tsuntsayen sama hikima. |
| 12 |
| Suka yi kira don taimako, amma Allah bai amsa ba, Saboda suna da girmankan mugaye. |
| 13 |
| Hakika Allah bai ji holoƙon kukansu ba, Allah Mai Iko Dukka kuwa bai kula da shi ba. |
| 14 |
| “Ayuba, kai wane ne da za ka ce ba ka gan shi ba? Da kake cewa ƙararka tana gabansa, Jiransa kake yi? |
| 15 |
| Yanzu fa saboda bai yi hukunci da fushinsa ba, Kamar kuma bai kula da laifi ba, |
| 16 |
| Ayuba, maganarka marar ma'ana ce, Ka yi ta maganganu marasa hikima.” |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/job/035.mp3
42
35