Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Sai Elihu ya ce, |
| 2 |
| “Ko kana tsammani wannan gaskiya ne? Kana cewa, ‘Ni mai adalci ne a gaban Allah.’ |
| 3 |
| Duk da haka kana tambayarsa cewa, ‘Wace riba nake da ita, kuma mene ne zan samu ta wurin ƙin yin zunubi?’ |
| 4 |
| “Zan so in ba ka amsa kai tare da abokanka. |
| 5 |
| Ku ɗaga kai ku dubi sama ku gani; ku dubi gizagizai a samanku. |
| 6 |
| In kun yi zunubi ta yaya wannan zai shafi Allah? In zunubanku sun yi yawa, me wannan zai yi masa? |
| 7 |
| In kuna da adalci, me kuka ba shi, ko kuma me ya karɓa daga hannunku? |
| 8 |
| Muguntarku takan shafi mutum kamar ku ne kaɗai, adalcinku kuma yakan shafi ’yan adam ne kaɗai. |
| 9 |
| “Mutane suna kuka don yawan zalunci; suna roƙo don taimako daga hannu mai ƙarfi. |
| 10 |
| Amma ba wanda ya ce, ‘Ina Allah wanda ya halicce ni, mai ba da waƙoƙi cikin dare, |
| 11 |
| wanda ya fi koya mana fiye da dabbobin duniya ya kuma sa muka fi tsuntsayen cikin iska hikima.’ |
| 12 |
| Ba ya amsawa lokacin da mutane suka yi kira don taimako domin girman kan mugaye. |
| 13 |
| Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi; Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu. |
| 14 |
| Ta yaya zai saurara sosai ko zai saurara lokacin da kake cewa ba ka ganinsa, cewa ka kawo ƙara a wurinsa kuma dole ka jira shi. |
| 15 |
| Kuma ka ce, ba ya ba da horo cikin fushinsa ko kaɗan ba ya kula da mugunta. |
| 16 |
| Saboda haka Ayuba ya buɗe baki yana magana barkatai; yana ta yawan magana ba tare da sani ba.” |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/job/035.mp3
42
35