|
| 1 |
|
| Elihu ya ci gaba da magana. |
|
| 2 |
|
| “Ka yi mini haƙuri kaɗan, ni kuwa zan nuna maka, Gama har yanzu ina da abin da zan faɗa in kāre Allah. |
|
| 3 |
|
| Zan tattaro ilimina daga nesa, In bayyana adalcin Mahaliccina. |
|
| 4 |
|
| Gaskiya nake faɗa ba ƙarya ba, Wanda yake da cikakken sani yana tare da kai. |
|
| 5 |
|
| “Ga shi kuwa, Allah Mai Girma, ba ya raina kowa, Shi mai girma ne, mai cikakkiyar basira. |
|
| 6 |
|
| Ba ya rayar da masu laifi, Amma yakan ba waɗanda ake tsananta wa halaliyarsu. |
|
| 7 |
|
| Yakan kiyaye waɗanda suke aikata gaskiya, Yakan kafa su har abada tare da sarakuna, A gadon sarauta, ya ɗaukaka su. |
|
| 8 |
|
| Amma idan aka ɗaure su da sarƙoƙi, Da kuma igiyar wahala, |
|
| 9 |
|
| Sa'an nan yakan sanar da su aikinsu Da laifofin da suke yi na ganganci. |
|
| 10 |
|
| Yakan sa su saurari koyarwa, Da umarnai, cewa su juya, su bar mugunta. |
|
| 11 |
|
| Idan suka kasa kunne suka bauta masa, Za su cika kwanakinsu da wadata, Shekarunsu kuma da jin daɗi. |
|
| 12 |
|
| Amma idan ba su kasa kunne ba, Za a hallaka su da takobi, Su mutu jahilai. |
|
| 13 |
|
| “Waɗanda ba su da tsoron Allah a zuciyarsu, Suna tanada wa kansu fushi, Ba su neman taimako sa'ad da ya ɗaure su. |
|
| 14 |
|
| Sukan yi mutuwar ƙuruciya, Sukan ƙare kwanakinsu da kunya. |
|
| 15 |
|
| Zai kuɓutar da waɗanda suke shan tsanani, Ta wurin tsananin da suke sha, Yakan buɗe kunnuwansu ta wurin shan wahala. |
|
| 16 |
|
| Allah ya tsamo ka daga cikin wahala, Ya kawo ka yalwataccen wuri inda ba matsi, Abincin da aka yi na addaras aka jera maka a kan tebur. |
|
| 17 |
|
| “Ka damu ƙwarai don ka ga an hukunta mugaye, Amma hukunci da adalci sun kama ka. |
|
| 18 |
|
| Ka lura kada ka bar hasalarka ta sa ka raina Allah, Kada kuma ka bar wahalar da kake sha ta sa ka ɓata da mai fansarka. |
|
| 19 |
|
| Kukanka ya iya raba ka da wahala, Ko kuwa dukan ƙarfin da kake da shi? |
|
| 20 |
|
| Kada ka ƙosa dare ya yi, Domin a lokacin nan ne mutane sukan watse, Kowa ya kama gabansa. |
|
| 21 |
|
| Ka lura kada ka rinjayu a kan aikata mugunta, Gama saboda haka kake shan wannan tsanani, Don a tsare ka daga aikata mugunta. |
|
| 22 |
|
| “Duba, Allah Maɗaukaki ne cikin ikonsa, Wa ya iya koyarwa kamarsa? |
|
| 23 |
|
| Ba wanda zai iya tsara wa Allah abin da zai yi, Wa ya isa ya ce masa ya yi kuskure? |
|
| 24 |
|
| “Ka tuna ka girmama aikinsa, Wanda mutane suke yabo. |
|
| 25 |
|
| Dukan mutane sun ga ayyukansa, Sun hango shi daga nesa. |
|
| 26 |
|
| Ga shi kuwa, Allah Maɗaukaki ne, Ba mu kuwa san iyakar ɗaukakarsa ba, Yawan shekarunsa ba su bincikuwa. |
|
| 27 |
|
| “Allah yakan sa ruwa ya zama tururi, Ya maishe shi ruwan sama, |
|
| 28 |
|
| Wanda yakan kwararo daga sama, Ya zubo wa ɗan adam a yalwace. |
|
| 29 |
|
| Wa zai iya gane yadda gizagizai suke shimfiɗe a sararin sama, Da tsawar da ake yi a cikinsu? |
|
| 30 |
|
| Ga shi, yakan baza waƙiya kewaye da shi, Yakan rufe ƙwanƙolin duwatsu. Zurfin teku yana nan da duhunsa. |
|
| 31 |
|
| Gama ta haka yakan shara'anta mutane, Yakan ba da abinci a yalwace. |
|
| 32 |
|
| Ya cika hannunsa da walƙiya, Yakan sa ta faɗa a kan abin da ya bārata. |
|
| 33 |
|
| Tsawarta tana nuna kasancewar Allah, Ko shanu sun san da zuwan hadiri.” |
|
|
|
|