|
| 1 |
|
| Elihu ya ci gaba, |
|
| 2 |
|
| “Ka ɗan ƙara haƙuri da ni kaɗan, zan kuma nuna maka cewa akwai sauran abubuwan da zan faɗa a madadin Allah. |
|
| 3 |
|
| Daga nesa na sami sanina; zan nuna cewa Mahaliccina shi mai gaskiya ne. |
|
| 4 |
|
| Abin da zan gaya maka ba ƙarya ba ne; mai cikakken sani yana tare da kai. |
|
| 5 |
|
| “Allah mai iko ne, amma ba ya rena mutane; shi mai girma ne cikin manufarsa. |
|
| 6 |
|
| Ba ya barin mugaye da rai sai dai yana ba waɗanda ake tsanantawa hakkinsu. |
|
| 7 |
|
| Ba ya fasa duban masu adalci; yana sa su tare da sarakuna yana ɗaukaka su har abada. |
|
| 8 |
|
| Amma in mutane suna daure da sarƙoƙi, ƙunci kuma ya daure su, |
|
| 9 |
|
| yana gaya musu abin da suka yi, cewa sun yi zunubi da girman kai. |
|
| 10 |
|
| Yana sa su saurari gyara yă kuma umarce su su tuba daga muguntarsu. |
|
| 11 |
|
| In sun yi biyayya suka bauta masa, za su yi rayuwa dukan kwanakinsu cikin wadata shekarunsu kuma cikin kwanciyar zuciya. |
|
| 12 |
|
| Amma in ba su saurara ba, za su hallaka da takobi kuma za su mutu ba ilimi. |
|
| 13 |
|
| “Waɗanda ba su da Allah a zuciyarsu su ne suke riƙe fushi; ko sa’ad da ya ba su horo, ba su neman taimakonsa. |
|
| 14 |
|
| Suna mutuwa tun suna matasa, cikin ƙazamar rayuwar karuwanci. |
|
| 15 |
|
| Amma yana kuɓutar da masu wahala; yana magana da su cikin wahalarsu. |
|
| 16 |
|
| “Yana so yă rinjaye ka daga haƙoran ƙunci, zuwa wuri mai sauƙi inda ba matsi zuwa teburinka cike da abincin da kake so. |
|
| 17 |
|
| Amma yanzu an cika ka da hukuncin da ya kamata a yi wa mugaye; shari’a da kuma gaskiya sun kama ka. |
|
| 18 |
|
| Ka yi hankali kada wani yă ruɗe ka da arziki; kada ka bar toshiya ta sa ka juya. |
|
| 19 |
|
| Dukiyarka ko dukan yawan ƙoƙarinka sun isa su riƙe ka su hana ka shan ƙunci? |
|
| 20 |
|
| Kada ka yi marmari dare yă yi, don a fitar da mutane daga gidajensu. |
|
| 21 |
|
| Ka kula kada ka juya ga mugunta, abin da ka fi so fiye da wahala. |
|
| 22 |
|
| “An ɗaukaka Allah cikin ikonsa. Wane ne malami kamar sa? |
|
| 23 |
|
| Wane ne ya nuna masa hanyar da zai bi, ko kuma wane ne ya ce masa, ‘Ba ka yi daidai ba?’ |
|
| 24 |
|
| Ka tuna ka ɗaukaka aikinsa, waɗanda mutane suka yaba a cikin waƙa. |
|
| 25 |
|
| Dukan ’yan adam sun gani; mutane sun hanga daga nesa. |
|
| 26 |
|
| Allah mai girma ne, ya wuce ganewarmu! Yawan shekarunsa ba su bincikuwa. |
|
| 27 |
|
| “Yana sa ruwa yă zama tururi yă zubo daga sama. |
|
| 28 |
|
| Gizagizai suna zubo da raɓarsu kuma ruwan sama yana zubowa ’yan adam a wadace. |
|
| 29 |
|
| Wane ne zai iya gane yadda ya shimfiɗa gizagizai yadda yake tsawa daga wurin zamansa? |
|
| 30 |
|
| Dubi yadda ya baza walƙiyarsa kewaye da shi, tana haskaka zurfin teku. |
|
| 31 |
|
| Haka yake mulkin al’ummai yana kuma tanada abinci a wadace. |
|
| 32 |
|
| Yana cika hannuwansa da walƙiya kuma yana ba ta umarni tă fāɗi a inda ya yi nufi. |
|
| 33 |
|
| Tsawarsa tana nuna cewa babbar iska da ruwa suna zuwa; ko shanu sun san da zuwansa. |
|
|
|
|