|
| 1 |
|
| “Wannan ya sa gabana ya fāɗi, zuciyata ta yi tsalle. |
|
| 2 |
|
| Ka saurara! Ka saurari rurin muryarsa, tsawar da take fita daga bakinsa. |
|
| 3 |
|
| Ya saki walƙiyarsa, a ƙarƙashin dukan sammai ya kuma aika ta ko’ina a cikin duniya. |
|
| 4 |
|
| Bayan wannan sai ƙarar rurinsa ta biyo; Ya tsawata da muryarsa mai girma. Sa’ad da ya sāke yin tsawa ba ya rage wani abu. |
|
| 5 |
|
| Muryar Allah tana tsawatawa a hanyoyi masu ban al’ajabi; yana yin manyan abubuwa waɗanda sun wuce ganewarmu. |
|
| 6 |
|
| Yakan ce wa dusar ƙanƙara, ‘Fāɗo a kan duniya,’ ya kuma ce wa ruwa, ‘Zubo da ƙarfi.’ |
|
| 7 |
|
| Domin dukan mutanen da ya halitta za su san aikinsa, ya hana kowane mutum yin wahalar aiki. |
|
| 8 |
|
| Dabbobi sun ɓoye; sun zauna cikin kogunansu. |
|
| 9 |
|
| Guguwa tana fitowa daga inda take, sanyi kuma daga iska mai sanyi. |
|
| 10 |
|
| Da numfashinsa Allah yana samar da ƙanƙara sai manyan ruwaye su zama ƙanƙara. |
|
| 11 |
|
| Yana cika gizagizai da lema; yana baza walƙiyarsa ta cikinsu. |
|
| 12 |
|
| Bisa ga bishewarsa suke juyawa a kan fuskar duniya, suna yin dukan abin da ya umarce su su yi. |
|
| 13 |
|
| Yana aiko da ruwa domin horon mutane, ko kuma don yă jiƙa duniya yă kuma nuna ƙaunarsa. |
|
| 14 |
|
| “Ka saurari wannan Ayuba; ka tsaya ka dubi abubuwan al’ajabi na Allah. |
|
| 15 |
|
| Ko ka san yadda Allah yake iko da gizagizai ya kuma sa walƙiyarsa ta haskaka? |
|
| 16 |
|
| Ko ka san yadda gizagizai suke tsayawa cik a sararin sama, waɗannan abubuwa al’ajabi na mai cikakken sani. |
|
| 17 |
|
| Kai mai sa kaya don ka ji ɗumi lokacin da iska mai sanyi take hurawa, |
|
| 18 |
|
| ko za ka iya shimfiɗa sararin sama tare da shi da ƙarfi kamar madubi? |
|
| 19 |
|
| “Gaya mana abin da ya kamata mu ce masa; ba za mu iya kawo ƙara ba domin duhunmu. |
|
| 20 |
|
| Ko za a gaya masa cewa ina so in yi magana? Ko wani zai nemi a haɗiye shi? |
|
| 21 |
|
| Yanzu ba wanda zai iya kallon rana, yadda take da haske a sararin sama bayan iska ta share ta. |
|
| 22 |
|
| Yana fitowa daga arewa da haske na zinariya, Allah yana zuwa da ɗaukaka mai ban al’ajabi. |
|
| 23 |
|
| Maɗaukaki ya fi ƙarfin ganewarmu, shi babban mai iko ne, mai gaskiya da babban adalci, ba ya cutar mutum. |
|
| 24 |
|
| Saboda haka, mutane suke girmama shi, ko bai kula da waɗanda suke gani su masu hikima ba ne?” |
|
|
|
|