|
| 1 |
|
| Ubangiji ya yi magana da Ayuba ta cikin guguwa. |
|
| 2 |
|
| “Wane ne wannan da yake ɓāta shawara Da maganganu marasa ma'ana? |
|
| 3 |
|
| Ka tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji, Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa. |
|
| 4 |
|
| A ina kake sa'ad da na aza harsashin gina duniya? Faɗa mini idan ka sani. |
|
| 5 |
|
| Wane ne ya zayyana kusurwoyinta? Hakika ka sani. Wane ne kuma ya auna ta? |
|
| 6 |
|
| A kan me aka kafa tushenta? Wa ya aza dutsen kan kusurwarta? |
|
| 7 |
|
| Sa'ad da taurarin asuba suka raira waƙa tare, Sai mala'iku duka suka yi sowa saboda murna. |
|
| 8 |
|
| “Wa ya yi wa teku iyaka Sa'ad da ta tumbatso daga zurfafa? |
|
| 9 |
|
| Sa'ad da na suturta ta da gizagizai, Na yi mata maɗauri da duhu ƙirin. |
|
| 10 |
|
| Na sa mata iyakoki, Na sa mata ƙyamare da ƙofofi, |
|
| 11 |
|
| Na ce mata, ‘Iyakar inda za ki tsaya ke nan, Ba za ki wuce ba. Nan raƙuman ruwanki masu tumbatsa za su tsaya.’ |
|
| 12 |
|
| “Ayuba, a dukan kwanakinka Ka taɓa umartar wayewar gari, Ko ka sa alfijir ya keto? |
|
| 13 |
|
| Da gari ya waye, Ka kawar da muguntar da ake yi da dare? |
|
| 14 |
|
| Yakan sāke kamar lakar da take ƙarƙashin hatimi, Yakan rine kamar riga. |
|
| 15 |
|
| Akan hana wa mugaye haske, Sa'ad da sukan ɗaga hannuwansu sama akan kakkarya su. |
|
| 16 |
|
| “Ko ka taɓa shiga cikin maɓuɓɓugan teku? Ka taɓa yin tafiya a cikin zurfin lallokin teku? |
|
| 17 |
|
| An taɓa nuna maka ƙofofin mutuwa? Ko kuwa ka taɓa ganin ƙofofin duhu ƙirin? |
|
| 18 |
|
| Ko ka san iyakar fāɗin duniya? Ka amsa mini in ka san dukan waɗannan. |
|
| 19 |
|
| “Ina hanya zuwa wurin da haske yake? A ina kuma duhu yake? |
|
| 20 |
|
| Ka san iyakarsa ko mafarinsa? |
|
| 21 |
|
| Ka sani, gama a lokacin nan an haife ka, Shekarunka kuwa suna da yawa. |
|
| 22 |
|
| “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara? Ko kuwa ka taɓa shiga rumbunan ajiyar ƙanƙara? |
|
| 23 |
|
| Na adana su ne don lokacin wahala, Domin ranar faɗa da ta yaƙi. |
|
| 24 |
|
| Ina hanya zuwa inda rana take fitowa, Ko kuma ta inda iskar gabas take hurowa ta māmaye ko'ina? |
|
| 25 |
|
| “Wa ya haƙa hanyar da ruwan sama mai kwararowa zai bi? Da kuma hanyar da gatarin aradu zai bi? |
|
| 26 |
|
| Wa ya kuma kawo ruwan sama a ƙasar da ba mutane, Da a cikin hamada inda ba kowa, |
|
| 27 |
|
| Don a shayar da zozayar ƙasa inda ba kowa, Har ta tsiro da ciyayi? |
|
| 28 |
|
| “Ruwan sama yana da mahaifi? Wa ya haifi ɗiɗɗigar raɓa? |
|
| 29 |
|
| Wace ce mahaifiyar ƙanƙara? Wace ce kuma ta haifi jaura? |
|
| 30 |
|
| Ruwa ya daskare ya yi ƙarfi kamar dutse, Teku ta daskare. |
|
| 31 |
|
| “Za ka iya ɗaure sarƙoƙin kaza-da-'ya'yanta? Ko ka iya kwance igiyoyin mafarauci-da-kare-da-zomo? |
|
| 32 |
|
| Za ka iya bi da yaneyanen sararin sama bisa ga fasalinsu? |
|
| 33 |
|
| Ka san ka'idodin sammai? Ko ka iya faɗar yadda suka danganta da duniya? |
|
| 34 |
|
| “Kana iya yi wa gizagizai tsawa, Don su kwararo ruwan sama, ya rufe ka? |
|
| 35 |
|
| Ka iya aikar walƙiyoyi su tafi, Sa'an nan su ce maka, ‘Ga mu mun zo?’ |
|
| 36 |
|
| Wa ya sa hikima a gizagizai, Ko kuma wa ya ba da ganewa ga kāsashi? |
|
| 37 |
|
| Akwai mai hikimar da zai iya ƙidaya gizagizai? Ko kuwa wa zai iya karkato da salkunan ruwan sammai, |
|
| 38 |
|
| Sa'ad da ƙura ta murtuke ta taru jingim, ta game kam? |
|
| 39 |
|
| “Ka iya farauto wa zakoki abinci? Ko ka ƙosar da yunwar sagarun zakoki, |
|
| 40 |
|
| Sa'ad da suke fako a kogwanninsu, Ko suna kwance suna jira a maɓoyarsu? |
|
| 41 |
|
| Wa yake tanada wa hankaka abincinsa, Sa'ad da 'ya'yansa suke kuka ga Allah, Suna kai da kawowa saboda rashin abinci?” |
|
|
|
|