|
| 1 |
|
| Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce, |
|
| 2 |
|
| “Wane ne wannan da yake ɓata mini shawarata da surutan wofi? |
|
| 3 |
|
| Ka sha ɗamara kamar namiji; zan yi maka tambaya, za ka kuwa amsa mini. |
|
| 4 |
|
| “Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya? Gaya mini, in ka sani. |
|
| 5 |
|
| Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani! Wane ne ya ja layin aunawa a kanta? |
|
| 6 |
|
| A kan me aka kafa tushenta, ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta, |
|
| 7 |
|
| yayinda taurarin safe suke waƙa tare dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki. |
|
| 8 |
|
| “Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi, lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki. |
|
| 9 |
|
| Lokacin da na yi wa gizagizai riga na kuma naɗe su a cikin duhu sosai, |
|
| 10 |
|
| sa’ad da na yi masa iyaka na sa masa ƙofofi da wurin kullewa. |
|
| 11 |
|
| Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai, ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya? |
|
| 12 |
|
| “Ko ka taɓa ba safiya umarni ko kuma ka sa asuba ta fito, |
|
| 13 |
|
| don ta kama gefen duniya ta kakkaɓe mugaye daga cikinta? |
|
| 14 |
|
| Ƙasa ta sāke siffa kamar laka da aka yi wa hatimi; ta fito a fili kamar riga. |
|
| 15 |
|
| An hana mugaye haskensu, hannun da suka ɗaga an karya shi. |
|
| 16 |
|
| “Ko ka taɓa tafiya zuwa maɓulɓulan teku, ko kuma ka taɓa zuwa cikin zurfin lungun teku? |
|
| 17 |
|
| Ko an taɓa nuna maka ƙofar mutuwa? Ko ka taɓa ganin ƙofar inuwar duhun mutuwa? |
|
| 18 |
|
| Ko ka gane fāɗin duniya? Gaya mini, in ka san wannan duka. |
|
| 19 |
|
| “Ina ne hanyar zuwa gidan haske? Kuma a ina duhu yake zama? |
|
| 20 |
|
| Ko za ka iya kai su wurarensu? Ka san hanyar zuwa wurin da suke zama? |
|
| 21 |
|
| Ba shakka ka sani, gama an riga an haife ka a lokacin! Ka yi shekaru da yawa kana rayuwa. |
|
| 22 |
|
| “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara ko ka taɓa ganin rumbunan ƙanƙara |
|
| 23 |
|
| waɗanda nake ajiya domin lokacin wahala, domin kwanakin yaƙi da faɗa? |
|
| 24 |
|
| Ina ne hanyar zuwa wurin da ake samun walƙiya, ko kuma inda daga nan ne ake watsa iskar gabas zuwa ko’ina cikin duniya? |
|
| 25 |
|
| Wane ne ya yanka hanyar wucewar ruwa, da kuma hanyar walƙiyar tsawa |
|
| 26 |
|
| don ba da ruwa a ƙasar da ba kowa a wurin jeji inda ba mai zama ciki |
|
| 27 |
|
| don a ƙosar da wurin da ya bushe a sa ciyawa ta tsiro a can? |
|
| 28 |
|
| Ruwan sama yana da mahaifi? Wa ya zama mahaifin raɓa? |
|
| 29 |
|
| Daga cikin wane ne aka haifi ƙanƙara? Wane ne ya haifi jaura daga sammai |
|
| 30 |
|
| lokacin da ruwa ya zama da ƙarfi kamar dutse, lokacin da saman ruwa ya daskare? |
|
| 31 |
|
| “Za ka iya daure kyakkyawar kaza da ’ya’yanta? Ko za ka iya kunce igiyoyin mafarauci da kare da zomo? |
|
| 32 |
|
| Za ka iya tattara taurari bisa ga lokacinsu ko kuma ka bi da beyar da ’ya’yanta zuwa waje? |
|
| 33 |
|
| Ka san dokokin sammai? Ko za ka iya faɗar dangantakar Allah da duniya? |
|
| 34 |
|
| “Za ka iya tsawata wa gizagizai ka kuma rufe kanka da ambaliyar ruwa? |
|
| 35 |
|
| Kai ne kake aika walƙiya da tsawa zuwa inda suke zuwa? Ko suna zuwa wurinka su ce, ‘Ga mu nan mun zo?’ |
|
| 36 |
|
| Wane ne yake cika zuciya da hikima ko kuma yake ba zuciya ganewa? |
|
| 37 |
|
| Wane ne yake da hikimar iya ƙirga gizagizai? Wane ne zai iya karkato bakunan tulunan sammai |
|
| 38 |
|
| sa’ad da ƙura ta yi yawa ta daskare a wuri ɗaya? |
|
| 39 |
|
| “Za ka iya farauto wa zakanya nama, ka kuma kawar wa zakoki yunwarsu. |
|
| 40 |
|
| Lokacin da suka kwanta cikin kogunansu, ko kuma lokacin da suke a wurin ɓuyansu? |
|
| 41 |
|
| Wane ne yake ba hankaka abinci lokacin da ’ya’yansa suke kuka ga Allah, kuma suna yawo don rashin abinci? |
|
|
: |
| 1 | | 2 | | 3 | | 4 | | 5 | | 6 | | 7 | | 8 | | 9 | | 10 | | 11 | | 12 | | 13 | | 14 | | 15 | | 16 | | 17 | | 18 | | 19 | | 20 | | 21 | | 22 | | 23 | | 24 | | 25 | | 26 | | 27 | | 28 | | 29 | | 30 | | 31 | | 32 | | 33 | | 34 | | 35 | | 36 | | 37 | | 38 | | 39 | | 40 | | 41 | 1
1
1 |
|
|---|
|
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/job/038.mp3
42
38