|
| 1 |
|
| “Ka san lokacin da awakan dutse suke haihuwa? Ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa? |
|
| 2 |
|
| Ka san ko watanni nawa suke yi kafin su haihu? Ka san lokacin haihuwarsu? |
|
| 3 |
|
| Ka san lokacin naƙudarsu, sa'ad da suke haihuwar 'ya'yansu, Lokacin da 'ya'yansu suke fita cikinsu? |
|
| 4 |
|
| 'Ya'yansu sukan yi ƙarfi su girma a fili cikin saura, Sukan yi tafiyarsu ba su komawa wurin iyayensu. |
|
| 5 |
|
| “Wa ya bar jakin jeji ya yi yadda yake so? Wa ya ɓalle dabaibayin jaki mai sauri, |
|
| 6 |
|
| Wanda na ba fili fetal ya zama gidansa, Da ƙasa mai gishiri a wurin zamansa? |
|
| 7 |
|
| Yakan yi wa hayaniyar birane ba'a, Ba ruwansa da tsawar masu kora. |
|
| 8 |
|
| Tsaunukan duwatsu ne wurin kiwonsa, A can yake neman kowane ɗanyen abu. |
|
| 9 |
|
| “Kutunkun ɓauna zai yarda ya yi maka aiki? Zai yarda ya kwana ɗaya a dangwalinka? |
|
| 10 |
|
| Ka iya ɗaure shi da igiya a kwarin kunya? Ko kuwa zai yi maka kaftu a fadamarka? |
|
| 11 |
|
| Za ka dogara gare shi saboda tsananin ƙarfinsa? Za ka kuma bar masa aikinka? |
|
| 12 |
|
| Ka gaskata zai komo, Ya kawo maka hatsi a masussukarka? |
|
| 13 |
|
| “Jimina takan karkaɗa fikafikanta da alfarma! Amma ba su ne gashin fikafikan ƙauna ba. |
|
| 14 |
|
| Jimina takan bar wa ƙasa ƙwayayenta, Ta bar ƙasa ta ɗumama su. |
|
| 15 |
|
| Takan manta wani ya iya taka su su fashe, Ya yiwu kuma wani naman jeji ya tattake su. |
|
| 16 |
|
| Takan yi wa 'ya'yanta mugunta, Sai ka ce ba nata ba ne, Ko da yake ta sha wahala a banza, Duk da haka ba ta damu ba. |
|
| 17 |
|
| Gama Allah bai ba ta hikima ba, Bai kuwa ba ta fahimi ba. |
|
| 18 |
|
| Amma sa'ad da ta sheƙa a guje, Takan yi wa doki maguji da mahayinsa dariya. |
|
| 19 |
|
| “Kai ka yi wa doki ƙarfinsa? Kai ne kuma ka daje wuyansa da geza? |
|
| 20 |
|
| Kai ne ka sa shi tsalle kamar ɗango? Kwarjinin firjinsa yana da bantsoro. |
|
| 21 |
|
| Yakan yi nishi a fadama, Yana murna saboda ƙarfinsa, A wurin yaƙi ba ya ja da baya, ba ya jin tsoron kibau. |
|
| 22 |
|
| Tsoro abin dariya ne a gare shi, bai damu ba. Ba ya ba da baya ga takobi, |
|
| 23 |
|
| Kibau na ta shillo a kansa, Māsu suna ta gilmawa a gabansa. |
|
| 24 |
|
| Da tsananin fushi da hasala yana kartar ƙasa, Da jin ƙarar ƙaho, sai ya yi ta zabura. |
|
| 25 |
|
| Sa'ad da aka busa ƙaho yana ce, ‘Madalla.’ Yakan ji warin yaƙi daga nesa, da hargowar sarakunan yaƙi da ihunsu. |
|
| 26 |
|
| “Ta wurin hikimarka ne shirwa take tashi, Ta buɗe fikafikanta ta nufi kudu? |
|
| 27 |
|
| Ta wurin umarninka ne gaggafa take tashi sama Ta yi sheƙarta can ƙwanƙoli? |
|
| 28 |
|
| A kan dutse take zaune, a can take gidanta, Cikin ruƙuƙin duwatsu. |
|
| 29 |
|
| Daga can takan tsinkayi abincinta Idanunta sukan hango shi tun daga nesa. |
|
| 30 |
|
| 'Yayanta sukan tsotsi jini, A inda kisassu suke, can take.” |
|
|
|
|