|
| 1 |
|
| “Ka san lokacin da awakin kan dutse suke haihuwa? Ko ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa? |
|
| 2 |
|
| Kana ƙirga watanni nawa suke yi kafin su haihu? Ka san lokacin da suke haihuwa? |
|
| 3 |
|
| Suna kwanciya su haifi ’ya’yansu; naƙudarsu ta ƙare bayan sun haihu. |
|
| 4 |
|
| ’Ya’yansu suna girma kuma suna girma cikin ƙarfi a jeji; sukan tafi ba su dawowa. |
|
| 5 |
|
| “Wane ne yake sakin jakin dawa yă bar shi? Wane ne yake kunce igiyoyinsu? |
|
| 6 |
|
| Na sa jeji yă zama gidansa ƙasar gishiri kuma ta zama wurin zamansa. |
|
| 7 |
|
| Yana dariyar hargitsin da yake faruwa a cikin gari; ba ya jin tsawar mai tuƙa shi. |
|
| 8 |
|
| Yana kiwo a kan tuddai don abincinsa yana neman kowane ɗanyen abu mai ruwan ciyawa. |
|
| 9 |
|
| “Ko ɓauna zai yarda yă zauna a wurin sa wa dabbobi abinci? Zai tsaya a ɗakin dabbobinka da dare? |
|
| 10 |
|
| Ko za ka iya daure shi da igiya a kwarin kunya? Zai yi maka buɗar gonarka? |
|
| 11 |
|
| Ko za ka dogara da shi don yawan ƙarfinsa? Za ka bar masa nauyin aikinka? |
|
| 12 |
|
| Ko za ka amince da shi yă kawo maka hatsinka gida yă tattara shi a masussuka? |
|
| 13 |
|
| “Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba. |
|
| 14 |
|
| Tana sa ƙwai nata a ƙasa kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa, |
|
| 15 |
|
| ba tă damu ko za a taka su a fasa su, ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su. |
|
| 16 |
|
| Tana tsananta wa ’ya’yanta kamar ba nata ba ba tă damu da wahalar da ta sha ba. |
|
| 17 |
|
| Gama Allah bai ba ta hikima ba ko kuma iya fahimta. |
|
| 18 |
|
| Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu tana yi wa doki da mai hawansa dariya. |
|
| 19 |
|
| “Ko kai ne kake ba doki ƙarfinsa kai kake rufe wuyansa da geza mai yawa? |
|
| 20 |
|
| Ko kai kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra, ba ya jin tsoro sai dai a ji tsoronsa. |
|
| 21 |
|
| Yana takawa da ƙarfi yana jin daɗin ƙarfinsa yana shiga filin yaƙi gabagadi. |
|
| 22 |
|
| Yana yi wa tsoro dariya ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi. |
|
| 23 |
|
| Kwari a baka yana lilo a gabansa kibiya da māshi suna wuce kansa. |
|
| 24 |
|
| Yana kartar ƙasa da ƙarfi; ba ya iya tsayawa tsab sa’ad da ya ji busar ƙaho. |
|
| 25 |
|
| Da jin ƙarar ƙaho sai ya ce, ‘Yauwa!’ Ya ji ƙanshin yaƙi daga nesa, da ihun shugabannin yaƙi. |
|
| 26 |
|
| “Ko ta wurin hikimarka ce shirwa take firiya take kuma baza fikafikanta zuwa kudu? |
|
| 27 |
|
| Ko da umarninka ne shaho yake firiya ya kuma yi sheƙarsa a can sama? |
|
| 28 |
|
| Yana zama a kan dutse yă zauna a wurin da dare; cikin duwatsu ne wurin zamansa. |
|
| 29 |
|
| Daga can yake neman abincinsa; idanunsa suna gani daga nesa. |
|
| 30 |
|
| ’Ya’yansa suna shan jini, inda akwai waɗanda aka kashe nan za a same shi.” |
|
|
|
|