|
| 1 |
|
| Elifaz ya yi magana. |
|
| 2 |
|
| “Ayuba, za ka ji haushi in na yi magana? Ba zan iya kannewa, in yi shiru ba. |
|
| 3 |
|
| Ka koya wa mutane da yawa, Ka kuma ƙarfafa hannuwan marasa ƙarfi. |
|
| 4 |
|
| Idan wani ya yi tuntuɓe, Ya gaji, ya rasa ƙarfi, Kalmominka suka ƙarfafa zuciyarsa, Har ya iya tsayawa kyam. |
|
| 5 |
|
| Yanzu naka lokacin wahala ya zo, Kai kuwa ka rikice, ka kasa ɗaurewa, |
|
| 6 |
|
| Kana yi wa Allah sujada, Ba wani laifi a zamanka, Ya kamata ka amince ka sa zuciya. |
|
| 7 |
|
| “Yanzu fa sai ka yi tunani. Ka faɗi bala'i ɗaya wanda ya taɓa fāɗa wa adalin mutum. |
|
| 8 |
|
| Na taɓa ganin mutane suna huɗe gonar mugunta, Suna shuka mugunta, Suka kuwa girbe mugunta. |
|
| 9 |
|
| A cikin fushinsa Allah yakan hallaka su kamar hadiri. |
|
| 10 |
|
| Mugaye sukan yi ruri suna gurnani kamar zakoki, Amma Allah yakan sa su yi tsit, Ya kakkarya haƙoransu. |
|
| 11 |
|
| Kamar zakoki da ba su da abin da za su kashe su ci, Haka nan za su mutu, 'ya'yansu kuwa su warwatse duka. |
|
| 12 |
|
| “Wata rana wani saƙo ya zo a hankali, Har da ƙyar nake iya ji, |
|
| 13 |
|
| Kamar wani irin mafarki mai razanarwa yake, Wanda ya hana ni jin daɗin barcina. |
|
| 14 |
|
| Na yi rawar jiki ina makyarkyata, Duk jikina yana ta ɓare-ɓare don tsoro. |
|
| 15 |
|
| Wata iska marar ƙarfi ta taɓa fuskata, Sai fatar jikina ta yanƙwane saboda fargaba. |
|
| 16 |
|
| Na ga wani abu can yana tsaye, Na zura ido, amma ban san kowane irin abu ba ne, Ina cikin wannan hali sai na ji murya, |
|
| 17 |
|
| Ta ce, ‘Mutum yana iya zama adali a gaban Allah? Akwai kuma wanda yake mai tsarki a gaban Mahaliccinsa? |
|
| 18 |
|
| Allah ba ya amince wa barorinsa na cikin sammai, Yakan sami laifi a wurin mala'ikunsa. |
|
| 19 |
|
| Ta ƙaƙa zai amince da talikinsa wanda aka yi da ƙasa, Abin da yake na ƙura, ana kuwa iya murƙushe shi kamar asu. |
|
| 20 |
|
| Mai yiwuwa ne mutum yana raye da safe Amma ya mutu ba a sani ba kafin maraice. |
|
| 21 |
|
| Duk abin da ya mallaka an ɗauke, Duk da haka ya mutu cikin rashin hikima.’ ” |
|
|
|
|