|
| 1 |
|
| Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa, |
|
| 2 |
|
| “In wani ya yi maka magana, za ka ji haushi? Amma wa zai iya yin shiru? |
|
| 3 |
|
| Ka tuna yadda ka yi wa mutane da yawa magana, yadda ka ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi. |
|
| 4 |
|
| Maganarka ta ƙarfafa waɗanda suka yi tuntuɓe; ka ƙarfafa gwiwoyin da suka rasa ƙarfinsu. |
|
| 5 |
|
| Amma yanzu wahala ta zo maka, sai ka karaya; wahala ta sa ka rikice. |
|
| 6 |
|
| Ashe bai kamata ka dogara ga Allahnka ba, amincinka kuma yă zama begenka? |
|
| 7 |
|
| “Ka duba ka gani yanzu. Wane marar laifi ne ya taɓa hallaka? Ko an taɓa hallaka masu adalci? |
|
| 8 |
|
| Na kula cewa waɗanda suke huɗa gonar mugunta, da waɗanda suke shuka mugunta, su ne suke girbe mugunta. |
|
| 9 |
|
| A sa’a ɗaya Allah yake hallaka su, cikin fushinsa yakan hallaka su. |
|
| 10 |
|
| Zakoki suna ruri suna gurnani; duk da haka an karya haƙoran manyan zakoki. |
|
| 11 |
|
| Zakoki suna mutuwa domin ba dabbar da za su kashe su ci, ’ya’yan zakanya kuma sun watse. |
|
| 12 |
|
| “Asirce aka gaya mini maganan nan, da ƙyar kunnuwana suka iya ji. |
|
| 13 |
|
| Cikin mafarki da tsakar dare, lokacin kowa yana zurfin barci, na sami saƙon nan. |
|
| 14 |
|
| Tsoro da fargaba suka kama ni har duk ƙasusuwan jikina suka yi ta rawa. |
|
| 15 |
|
| Wani iska ya taɓa mini fuska, sai tsigar jikina ta tashi. |
|
| 16 |
|
| Ya tsaya cik, amma ban iya sani ko mene ne ba. Wani abu ya tsaya a gabana, na kuma ji murya. |
|
| 17 |
|
| ‘Ko zai yiwu mutum yă fi Allah adalci, ko kuma mutum yă fi wanda ya halicce shi tsarki? |
|
| 18 |
|
| In Allah bai yarda da bayinsa ba, in ya sami mala’ikunsa da laifi, |
|
| 19 |
|
| to, su wane ne mutane masu zama a gidan da aka yi da laka, waɗanda da ƙura aka yi harsashensu, waɗanda za a iya murƙushe su kamar asu! |
|
| 20 |
|
| Tsakanin safe da yamma mai yiwuwa ne ragargaza su; farat ɗaya, su mutu har abada. |
|
| 21 |
|
| Ba a tuge igiyar tentinsu, don su mutu ba tare da hikima ba?’ |
|
|
|
|