|
| 1 |
|
| Ubangiji ya yi wa Ayuba magana. |
|
| 2 |
|
| “Mai neman sa wa wani laifi ya jā da Mai Iko Dukka? Wanda yake gardama da Allah, bari ya ba da amsa.” |
|
| 3 |
|
| Ayuba ya amsa wa Ubangiji ya ce, |
|
| 4 |
|
| “Ai, ni ba a bakin kome nake ba, Wace amsa zan ba ka? Na rufe bakina na yi gam. |
|
| 5 |
|
| Ai, na riga na yi magana sau ɗaya, har ma sau biyu, Ba zan amsa ba, ba zan ƙara cewa kome ba.” |
|
| 6 |
|
| Sa'an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba daga cikin guguwa, ya ce, |
|
| 7 |
|
| “Tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji, Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa. |
|
| 8 |
|
| Kai kanka za ka sa mini laifi? Za ka kā da ni don kai ka barata? |
|
| 9 |
|
| Kana da ƙarfi kamar na Allah? Kana iya tsawa da murya kamar tasa? |
|
| 10 |
|
| “Ka caɓa ado da kwarjini da ɗaukaka, Ka yafa daraja da maƙami. |
|
| 11 |
|
| Ka kwararar da rigyawar fushinka, Ka dubi dukan wanda yake alfarma, a wulakance. |
|
| 12 |
|
| Ka dubi dukan wanda yake alfarma ka ƙasƙantar da shi, Ka tattake mugaye a inda suke. |
|
| 13 |
|
| Dukansu ka binne su a ƙasa, Ka ɗaure fuskokinsu, ka jefa su a lahira. |
|
| 14 |
|
| Sa'an nan ni kaina kuma zan sanar da kai, Cewa da hannun damanka za ka yi nasara. |
|
| 15 |
|
| “Ga dorina wanda ni na halicce ta, Kamar yadda na halicce ka, Tana cin ciyawa kamar sa. |
|
| 16 |
|
| Ga shi, ƙarfinta yana cikin ƙugunta, Ikonta yana cikin tsakar cikinta. |
|
| 17 |
|
| Na yi mata wutsiya miƙaƙƙiya, mai ƙarfi kamar itacen al'ul, Jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe wuri ɗaya |
|
| 18 |
|
| Ƙasusuwanta bututun tagulla ne, Gaɓoɓinta kamar sandunan ƙarfe ne. |
|
| 19 |
|
| “Ita ce ta farko cikin ayyukan Allah, Sai Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkararta da takobi! |
|
| 20 |
|
| Gama duwatsu suke ba ta abinci, A inda dukan namomin jeji suke wasa. |
|
| 21 |
|
| Takan kwanta a inuwar ƙaddaji, Ta ɓuya a cikin iwa, da a fadama. |
|
| 22 |
|
| Gama inuwar da take rufe ta ta ƙaddaji ce, Itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta. |
|
| 23 |
|
| Ga shi, ba ta jin tsoron tumbatsar kogi, A natse take, ko da ta bakinta rigyawar Urdun take wucewa. |
|
| 24 |
|
| Akwai wanda zai iya kama ta da ƙugiya, Ko ya sa mata asirka?” |
|
|
|
|