|
| 1 |
|
| Ubangiji ya ce wa Ayuba, |
|
| 2 |
|
| “Mai neman sa wa wani laifi zai iya ja da Maɗaukaki? Bari mai tuhumar Allah yă amsa masa.” |
|
| 3 |
|
| Sai Ayuba ya amsa wa Ubangiji, |
|
| 4 |
|
| “Ai, ni ba a bakin kome nake ba ne, ta yaya zan iya amsa maka? Na rufe bakina da hannuna. |
|
| 5 |
|
| Na yi magana sau ɗaya amma ba ni da amsa, sau biyu, amma ba zan ƙara cewa kome ba.” |
|
| 6 |
|
| Sa’an nan Ubangiji ya yi wa Ayuba magana ta cikin guguwa, |
|
| 7 |
|
| “Ka tashi tsaye ka tsaya da ƙarfi kamar namiji; zan yi maka tambaya kuma za ka amsa mini. |
|
| 8 |
|
| “Ko za ka ƙi yarda da shari’ata? Za ka ba ni laifi don ka nuna kai marar laifi ne? |
|
| 9 |
|
| Ko hannunka irin na Allah ne, kuma ko muryarka za tă iya tsawa kamar ta Allah? |
|
| 10 |
|
| Sai ka yi wa kanka ado da ɗaukaka da girma, ka yafa daraja da muƙami. |
|
| 11 |
|
| Ka saki fushinka, ka dubi dukan wani mai girman kai ka wulaƙanta shi. |
|
| 12 |
|
| Ka dubi duk wani mai girman kai ka ƙasƙantar da shi, ka tattake mugaye a inda ka tsaya. |
|
| 13 |
|
| Ka bizne su duka tare ka rufe fuskokinsu a cikin kabari. |
|
| 14 |
|
| Sa’an nan ni kaina zan shaida maka cewa hannun damanka zai iya cetonka. |
|
| 15 |
|
| “Dubi dorina, wadda na halicce ku tare kuma ciyawa take ci kamar sa. |
|
| 16 |
|
| Ga shi ƙarfinta yana a ƙugunta ikonta yana cikin tsokar cikinta. |
|
| 17 |
|
| Wutsiyarta tana da ƙarfi kamar itacen al’ul; jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe a wuri ɗaya. |
|
| 18 |
|
| Ƙasusuwanta bututun tagulla ne, haƙarƙarinta kamar sandunan ƙarfe. |
|
| 19 |
|
| Tana ta farko cikin ayyukan Allah, Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkarar ta da takobi. |
|
| 20 |
|
| Tuddai su suke tanada mata abinci a inda duk namun jeji suke wasa. |
|
| 21 |
|
| Tana kwanciya a ƙarƙashin inuwar itacen lotus ta ɓuya cikin kyauro da fadama. |
|
| 22 |
|
| Inuwa ta rufe ta da ƙaddaji, itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta. |
|
| 23 |
|
| Sa’ad da kogi ya cika yana hauka, ba tă damu ba; ba abin da zai same ta ko da a gaban bakinta Urdun yake wucewa. |
|
| 24 |
|
| Ko akwai wanda zai iya kama ta ba ta kallo, ko kuma a kama ta da tarko a huda hancinta? |
|
|
|
|