|
| 1 |
|
| “Ko za ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kamar kifi ko kuma ka daure harshenta da igiya? |
|
| 2 |
|
| Za ka iya sa igiya a cikin hancinta ko kuma ka huda muƙamuƙanta da ƙugiya? |
|
| 3 |
|
| Za tă ci gaba da roƙonka ka yi mata jinƙai? Ko za tă yi maka magana a hankali? |
|
| 4 |
|
| Za tă yi yarjejjeniya da kai don ka ɗauke ta tă zama baiwa gare ka dukan kwanakin ranta? |
|
| 5 |
|
| Za ka yi wasa da ita kamar yadda za ka yi da tsuntsu? Ko za ka daure ta da tsirkiya domin bayinka mata? |
|
| 6 |
|
| ’Yan kasuwa za su saye ta ko za su raba ta a tsakaninsu? |
|
| 7 |
|
| Ko za ka iya huda fatarta da kibiya ka kuma huda kansa da māsu? |
|
| 8 |
|
| In ka ɗora hannunka sau ɗaya a kanta za ka tuna da yaƙin da ba za ka sāke yi ba! |
|
| 9 |
|
| Duk ƙoƙarin kama ta banza ne; ganin ta kawai abin tsoro ne. |
|
| 10 |
|
| Ba wanda ya isa yă tsokane ta. Wane ne kuma ya isa yă yi tsayayya da ni? |
|
| 11 |
|
| Wane ne yake bi na bashi da dole in biya? Duk abin da yake ƙarƙashin sama nawa ne. |
|
| 12 |
|
| “Ba zan daina magana game da gaɓoɓinta ba ƙarfinta da kuma kyan kamanninta ba. |
|
| 13 |
|
| Wa zai iya tuɓe mata mayafinta? Wa zai iya shiga tsakanin ɓawonta. |
|
| 14 |
|
| Wa zai iya buɗe ƙofofin bakinta? Haƙoranta ma abin tsoro ne? |
|
| 15 |
|
| An rufe bayanta da jerin garkuwoyi aka manne su sosai. |
|
| 16 |
|
| Suna kurkusa da juna yadda da ƙyar iska take iya wucewa tsakani. |
|
| 17 |
|
| An haɗa su da juna sun mannu da juna kuma ba za a iya raba su ba. |
|
| 18 |
|
| Numfashinta yana fitar da wuta; idanunta kamar hasken zuwan safe. |
|
| 19 |
|
| Wuta tana fitowa daga bakinta; tartsatsin wuta suna fitowa, |
|
| 20 |
|
| Hayaƙi yana fitowa daga hancinta kamar daga tukunya mai tafasa a kan wutar itace. |
|
| 21 |
|
| Numfashinta yana sa garwashi yă kama wuta, harshen wuta yana fita daga bakinta. |
|
| 22 |
|
| Akwai ƙarfi a cikin wuyanta; razana tana wucewa a gabanta. |
|
| 23 |
|
| Namanta yana da kauri a manne da juna; naman yana da tauri ba ya matsawa. |
|
| 24 |
|
| Ƙirjinta yana da ƙarfi kamar dutse, da ƙarfi kamar dutsen niƙa. |
|
| 25 |
|
| Sa’ad da ta tashi, manya suna tsorata; suna ja da baya. |
|
| 26 |
|
| Takobi ba ta iya yankanta, kibiya ko māshi ba sa iya huda ta. |
|
| 27 |
|
| Ƙarfe kamar kara ne a wurinta tagulla kuma kamar ruɓaɓɓen katako ne a wurinta. |
|
| 28 |
|
| Māsu ba su sa ta tă gudu; jifar majajjawa kamar na ciyawa ne gare ta. |
|
| 29 |
|
| Kulki a gare ta kamar ciyawa ne, tana dariyar wucewar māshi. |
|
| 30 |
|
| Cikinta yana rufe a ɓawo masu ƙarfi, tana kabtar ƙasa in tana tafiya. |
|
| 31 |
|
| Tana sa zurfin kogi yă tafasa kamar tukunya, ta kuma sa teku yă zama kamar tukunyar man shafawa. |
|
| 32 |
|
| A bayanta ya bar haske kamar zurfin ruwan da yana kumfa. |
|
| 33 |
|
| Ba wani abu kamar ta a duniya, halitta marar tsoro. |
|
| 34 |
|
| Tana rena duk masu girman kai. Ita take mulki kan duk masu girman kai.” |
|
|
|
|