|
| 1 |
|
| “Ka yi kira, ya Ayuba, ka gani, ko wani zai amsa! Akwai wani mala'ika da za ka juya zuwa gare shi? |
|
| 2 |
|
| Ba shi da amfani ka dami kanka Har ka mutu, saboda tsarguwa, gama wannan wawanci ne, Da aikin rashin hankali. |
|
| 3 |
|
| Na ga waɗansu wawaye waɗanda ake gani kamar suna zaune lafiya, Amma nan da nan sai na la'anci gidajensu. |
|
| 4 |
|
| Ko kaɗan, 'ya'yansu maza ba za su taɓa zama lafiya ba. Ba wanda zai tsaya musu a ɗakin shari'a. |
|
| 5 |
|
| Mayunwata za su ci amfanin gonar wawa, Har da hatsin da yake girma cikin ƙayayuwa, Waɗanda suke jin ƙishirwa za su ji ƙyashin dukiyarsa. |
|
| 6 |
|
| Zunubi ba ya tsirowa daga ƙasa, Haka ma wahala ba ta tsirowa daga ƙasa. |
|
| 7 |
|
| Ai, an haifi mutum domin wahala ne, Tabbatacce ne kamar yadda tartsatsin wuta suke tashi. |
|
| 8 |
|
| “In da ni ne kai, da sai in juya wurin Allah, In kai ƙarata a wurinsa. |
|
| 9 |
|
| Ba za mu iya fahimtar manyan abubuwa da yake yi ba, Al'ajabansa kuwa ba su da iyaka. |
|
| 10 |
|
| Yakan aiko da ruwan sama, Ya shayar da gonaki. |
|
| 11 |
|
| I, Allah ne yake ɗaukaka masu tawali'u, Shi yake kuɓutar da dukan waɗanda suke makoki. |
|
| 12 |
|
| Yakan birkitar da shirye-shiryen masu wayo. |
|
| 13 |
|
| Yakan sa wa masu wayo tarko cikin dabarunsu, Har ba za su yi nasara a dukan abin da suke yi ba. |
|
| 14 |
|
| Da rana sukan yi karo da duhu, Ko da tsakar rana ma lalube suke kamar ana duhu. |
|
| 15 |
|
| Amma Allah yakan ceci matalauta daga mutuwa, Yakan kuma ceci masu bukata daga zalunci. |
|
| 16 |
|
| Yakan sa matalauta su sa zuciya, Ya sa mugaye su yi shiru. |
|
| 17 |
|
| “Mai farin ciki ne mutumin da Allah ya hora, Kada ka tsargu sa'ad da ya tsauta maka. |
|
| 18 |
|
| Allah yakan yi maganin raunin da ya yi maka, Ciwon da ya ji maka da hannunsa, Da hannunsa yakan warkar. |
|
| 19 |
|
| Yakan tsare ka daga cuta sau shida har sau bakwai, Ba muguntar da za ta taɓa ka. |
|
| 20 |
|
| Yakan kiyaye ka da rai a lokacin yunwa, A yaƙi kuma yakan tsare ka daga mutuwa. |
|
| 21 |
|
| Allah yakan kuɓutar da kai daga ƙarairayi da ɓata suna, Yakan cece ka daga hallaka. |
|
| 22 |
|
| Aikin kama-karya da yunwa za su zama abin dariya a gare ka, Ba kuwa za ka ji tsoron namomin jeji ba. |
|
| 23 |
|
| Ba za a sami duwatsu a gonakin da kake nomawa ba, Mugayen namomin jeji ba za su far maka ba. |
|
| 24 |
|
| Sa'an nan za ka zauna lafiya a alfarwanka, A sa'ad da ka dubi tumakinka, za ka tarar suna nan lafiya. |
|
| 25 |
|
| 'Ya'yanka za su yi yawa kamar ciyawa, Kamar yadda alkama take a lokacin kakarta. |
|
| 26 |
|
| Haka kai ma za ka rayu, har ka tsufa da kyakkyawan tsufa. |
|
| 27 |
|
| Kai, Ayuba, mun koyi wannan don mun daɗe muna nazari, Gaskiya ce, don haka ka yarda da wannan.” |
|
|
|
|