|
| 1 |
|
| “Ka yi kira in kana so, amma wa zai amsa maka? Wurin waɗanne tsarkaka za ka juya? |
|
| 2 |
|
| Fushi yana kashe wawa, ƙyashi kuma yana kashe marar azanci. |
|
| 3 |
|
| Ni ma na ga wawa yana cin gaba, amma nan da nan gidansa ya zama la’ananne. |
|
| 4 |
|
| ’Ya’yansa suna cikin hatsari, ba wanda zai tsaya musu a gaban alƙali, |
|
| 5 |
|
| mayunwata sun kwashe girbinsa, har abubuwan da suke cikin ƙaya, masu jin ƙishirwa kuma suna zuba ido ga dukiyarsa. |
|
| 6 |
|
| Gama ba daga cikin ƙasa wahala take fitowa ba, ko kuma bala’i daga ƙasa. |
|
| 7 |
|
| Duk da haka an haifi mutum don wahala ne, kamar yadda ba shakka tartsatsin wuta yake tashi. |
|
| 8 |
|
| “Amma da a ce ni ne, da zan roƙi Allah; zan gaya masa damuwata. |
|
| 9 |
|
| Yana yin abubuwan al’ajabi waɗanda ba a ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a ƙirgawa. |
|
| 10 |
|
| Yana zuba ruwan sama a ƙasa; yana zuba ruwa a gonaki. |
|
| 11 |
|
| Yana ɗaukaka masu sauƙinkai, yana kāre waɗanda suke makoki. |
|
| 12 |
|
| Yana dagula shirye-shiryen masu wayo don kada su yi nasara cikin abubuwan da suke shirin yi. |
|
| 13 |
|
| Yana kama masu wayo cikin wayonsu, yana kawar da shirye-shiryensu ba za su yi nasara ba. |
|
| 14 |
|
| Da rana sukan yi karo da duhu; da rana ma suna lallube kamar a duhun dare suke. |
|
| 15 |
|
| Yana ceton matalauta daga takobin da za tă kashe su da shi; yana cetonsu daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi. |
|
| 16 |
|
| Saboda haka matalauta suna da bege, rashin gaskiya kuma ta yi shiru. |
|
| 17 |
|
| “Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure; saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki. |
|
| 18 |
|
| Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon; ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi. |
|
| 19 |
|
| Zai cece ka daga bala’o’i guda shida; har bakwai ma ba abin da zai same ka. |
|
| 20 |
|
| Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi. |
|
| 21 |
|
| Zai kāre ka daga ɓata suna, kuma ba ka bukata ka ji tsoro in hallaka ta zo. |
|
| 22 |
|
| Za ka yi wa hallaka da yunwa dariya; kuma ba ka bukata ka ji tsoron manyan namun jeji. |
|
| 23 |
|
| Gama za ka zauna lafiya da duwatsu a gonaki, kuma manyan namun jeji za su yi zaman salama da kai. |
|
| 24 |
|
| Za ka zauna lafiya a cikin tenti naka, za ka ƙirga kayanka za ka samu kome na nan. |
|
| 25 |
|
| Za ka san cewa ’ya’yanka za su zama da yawa, zuriyarka kuma kamar ciyawa a ƙasa. |
|
| 26 |
|
| Za ka yi kyakkyawan tsufa kafin ka mutu, kamar yadda ake tara dammuna a lokacin girbi. |
|
| 27 |
|
| “Mun yi nazarin wannan, kuma gaskiya ne. Saboda haka ka ji, ka kuma yi amfani da shi.” |
|
|
|
|