|
| 1 |
|
| Sa’an nan Ayuba ya amsa, |
|
| 2 |
|
| “Da kawai za a iya auna wahalata a kuma sa ɓacin raina a ma’auni! |
|
| 3 |
|
| Ba shakka da sun fi yashin teku nauyi, shi ya sa nake magana haka. |
|
| 4 |
|
| Kibiyoyin Maɗaukaki suna a kaina, ruhuna yana shan dafinsa; fushin Allah ya sauka a kaina. |
|
| 5 |
|
| Jaki yakan yi kuka sa’ad da ya sami ciyawar ci, ko saniya takan yi kuka in ta sami abincinta? |
|
| 6 |
|
| Akan cin abinci marar ɗanɗano ba tare da an sa gishiri ba, ko akwai wani ƙanshin daɗi a cikin farin ruwan ƙwai? |
|
| 7 |
|
| Na ƙi in taɓa shi; irin wannan abinci zai sa ni rashin lafiya. |
|
| 8 |
|
| “Kash, da ma Allah zai ba ni abin da nake fatar samu, da ma Allah zai biya mini bukatata, |
|
| 9 |
|
| wato, Allah yă kashe ni, yă miƙa hannunsa yă yanke raina! |
|
| 10 |
|
| Da sai in ji daɗi duk zafin da nake sha ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba. |
|
| 11 |
|
| “Wane ƙarfi nake da shi, har da zan ci gaba da sa zuciya? Wane sa zuciya ne zai sa in yi haƙuri? |
|
| 12 |
|
| Da ƙarfin dutse aka yi ni ne? Ko jikina tagulla ne? |
|
| 13 |
|
| Ina da wani ikon da zan iya taimakon kai na ne, yanzu da aka kore nasara daga gare ni? |
|
| 14 |
|
| “Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki ya rabu ta tsoron Maɗaukaki. |
|
| 15 |
|
| Amma ’yan’uwana sun nuna ba zan iya dogara gare su ba, kamar rafin da yakan bushe da rani, |
|
| 16 |
|
| kamar rafin da yakan cika a lokacin ƙanƙara, yă kuma kumbura kamar ƙanƙarar da ta narke, |
|
| 17 |
|
| amma da rani sai yă bushe, lokacin zafi ba a samun ruwa yana gudu a wurin. |
|
| 18 |
|
| Ayari sukan bar hanyarsu; sukan yi ta neman wurin da za su sami ruwa, su kāsa samu har su mutu. |
|
| 19 |
|
| Ayarin Tema sun nemi ruwa, matafiya ’yan kasuwa Sheba sun nema cike da begen samu. |
|
| 20 |
|
| Ransu ya ɓace, domin sun sa zuciya sosai; sa’ad da suka kai wurin kuwa ba su sami abin da suka sa zuciyar samu ba. |
|
| 21 |
|
| Yanzu kuma kun nuna mini ba ku iya taimako; kun ga abin bantsoro kuka tsorata. |
|
| 22 |
|
| Ko na taɓa cewa, ‘Ku ba da wani abu a madadina, ko na roƙe ku, ku ba da wani abu domina daga cikin dukiyarku, |
|
| 23 |
|
| ko kuma kun taɓa kuɓutar da ni daga hannun maƙiyina, ko kun taɓa ƙwato ni daga hannun marasa kirki’? |
|
| 24 |
|
| “Ku koya mini, zan yi shiru; ku nuna mini inda ban yi daidai ba. |
|
| 25 |
|
| Faɗar gaskiya tana da zafi! Amma ina amfanin gardamar da kuke yi? |
|
| 26 |
|
| Ko kuna so ku gyara abin da na faɗi ne, ku mai da magana wanda yake cikin wahala ta zama ta wofi? |
|
| 27 |
|
| Kukan yi ƙuri’a a kan marayu ku kuma sayar da abokinku. |
|
| 28 |
|
| “Amma yanzu ku dube ni da kyau, zan yi muku ƙarya ne? |
|
| 29 |
|
| Ku bi a hankali, kada ku ɗora mini laifi; ku sāke dubawa, gama ba ni da laifi. |
|
| 30 |
|
| Ko akwai wata mugunta a bakina? Bakina ba zai iya rarrabewa tsakanin gaskiya da ƙarya ba? |
|
|
|
|