Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| “Kamar kamen soja na tilas, Haka zaman 'yan adam take, Kamar zaman mai aikin bauta. |
| 2 |
| Kamar bawa ne wanda yake sa zuciya ga inuwa mai sanyi, Kamar ma'aikaci wanda yake sa zuciya ga lokacin biya. |
| 3 |
| Wata da watanni ina ta aikin banza, Kowane dare ɓacin rai yake kawo mini. |
| 4 |
| Sa'ad da na kwanta barci, sai daren ya daɗa tsawo In yi ta jujjuyawa duk dare, in ƙosa gari ya waye. |
| 5 |
| Jikina cike yake da tsutsotsi, Ƙuraje duka sun rufe shi, Daga miyakuna mugunya tana ta zuba. |
| 6 |
| Kwanakina sun wuce ba sa zuciya, Sun wuce da sauri kamar ƙoshiyar saƙa. |
| 7 |
| “Ka tuna, ya Ubangiji, raina iska ne kawai, Farin cikina ya riga ya ƙare. |
| 8 |
| Kuna ganina yanzu, amma ba za ku sāke ganina ba. Idan kuka neme ni, za ku tarar ba na nan. |
| 9 |
| Kamar girgijen da yake bajewa ya tafi, Haka nan mutum yake mutuwa. |
| 10 |
| Ba kuwa zai ƙara komowa ba, Mutanen da suka san shi, duka za su manta da shi. |
| 11 |
| A'a, ko kaɗan ba zan yi shiru ba! Haushi nake ji, zuciyata ta ɓaci, Dole ne in yi magana. |
| 12 |
| “Ya Ubangiji, don me ka sa ni a waƙafi? Kana tsammani ni dodon ruwa ne? |
| 13 |
| Na kwanta ina ƙoƙari in huta, Ina neman taimako don azabar da nake sha. |
| 14 |
| Amma kai kana firgita ni da mafarkai, Kana aiko mini da wahayi da ganegane, |
| 15 |
| Har nakan fi so a rataye ni, Gara in mutu da in rayu a wannan hali. |
| 16 |
| Na fid da zuciya. Na gaji da rayuwa. Ku rabu da ni. Rayuwa ba ta da wata ma'ana. |
| 17 |
| “Ya Ubangiji, me ya sa mutum yake da daraja haka a gare ka? Me ya sa kake lura da abin da yake yi? |
| 18 |
| Kakan dube shi kowace safiya. Kana jarraba shi a kowane daƙiƙa. |
| 19 |
| Ba za ka ko ɗan kawar da kai ba, Don in samu in haɗiye yau? |
| 20 |
| Ko na yi zunubi ina ruwanka, Kai mai ɗaure mutane? Me ya sa ka maishe ni abin bārata? Ni wani babban kaya mai nauyi ne a gare ka? |
| 21 |
| Ba za ka iya gafarta mini zunubina ba? Ba za ka kawar da kai ga muguntar da na aikata ba? Ba da daɗewa ba zan rasu in koma a ƙura, Lokacin da ka neme ni ba za ka same ni ba.” |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/job/007.mp3
42
7