|
| 1 |
|
| “Mutum bai sha wahalar aiki ba a duniya? Rayuwarsa ba kamar ta wanda aka yi hayarsa ba ne? |
|
| 2 |
|
| Kamar yadda bawa yakan jira yamma ta yi, ko kuma kamar yadda wanda aka yi hayarsa yakan jira a biya shi kuɗin aikin da ya yi. |
|
| 3 |
|
| Saboda haka rabona shi ne watanni na zama banza, kowane dare kuwa sai ɓacin rai nake samu. |
|
| 4 |
|
| Lokacin da na kwanta ina tunani, ‘Har sai yaushe zan tashi?’ Gari ya ƙi wayewa, ina ta jujjuyawa har safe. |
|
| 5 |
|
| Jikina duk tsutsotsi da ƙuraje sun rufe shi, fatar jikina ta ruɓe tana fitar da ruwan miki. |
|
| 6 |
|
| “Kwanakina suna wucewa da sauri, fiye da yadda ƙoshiyar masaƙa take wucewa da sauri, za su kawo ga ƙarshe ba bege. |
|
| 7 |
|
| Ka tuna, ya Allah, raina numfashi ne kawai; idanuna ba za su taɓa sāke ganin farin ciki ba. |
|
| 8 |
|
| Idanun da suke ganina yanzu ba za su sāke ganina ba; za ku neme ni amma ba za ku same ni ba. |
|
| 9 |
|
| Kamar yadda girgije yakan ɓace yă tafi, haka mutum yake shige zuwa kabari ba kuwa zai dawo ba. |
|
| 10 |
|
| Ba zai taɓa zuwa gidansa ba; ba za a sāke san da shi ba. |
|
| 11 |
|
| “Saboda haka ba zan yi shiru ba; zan yi magana cikin ɓacin raina, zan nuna ɓacin raina cikin ruhu, cikin ƙuncin raina. |
|
| 12 |
|
| Ni teku ne, ko kuwa dodon ruwa, don me kake tsaro na? |
|
| 13 |
|
| Lokacin da nake zato zan sami salama in na kwanta a gadona don in huta, |
|
| 14 |
|
| duk da haka kana ba ni tsoro da mafarke-mafarke, kana tsorata ni da wahayi. |
|
| 15 |
|
| Na gwammace a shaƙe ni in mutu maimakon in kasance cikin wannan jiki. |
|
| 16 |
|
| Ba na so in zauna da rai; ba zan rayu ba har abada. Ku rabu da ni; rayuwata ba ta da amfani. |
|
| 17 |
|
| “Mene ne mutum har da ka kula da shi haka, har ka mai da hankali a kansa, |
|
| 18 |
|
| har kake duba shi kowace safiya, kake kuma gwada shi koyaushe? |
|
| 19 |
|
| Ba za ka ɗan daina kallo na ba ko ka rabu da ni na ɗan lokaci? |
|
| 20 |
|
| In na yi zunubi, me na yi maka, kai mai lura da mutane? Don me ka sa ni a gaba? Na zame maka kaya mai nauyi ne? |
|
| 21 |
|
| Me ya sa ba za ka gafarta mini laifofina ba? Gama na kusa kwantawa cikin ƙasa; za ka neme ni, amma ba za ka same ni ba.” |
|
|
|
|