|
| 1 |
|
| Sai Bildad ya yi magana. |
|
| 2 |
|
| “Ka gama maganganunka marasa kan gado duka? |
|
| 3 |
|
| Allah bai taɓa yin danniya ba, Bai kuma taɓa fāsa aikata abin da yake daidai ba. |
|
| 4 |
|
| Lalle 'ya'yanka sun yi wa Allah zunubi, Don haka ya hukunta su yadda ya cancanta. |
|
| 5 |
|
| Amma sai ka juyo ka yi roƙo ga Allah Maɗaukaki. |
|
| 6 |
|
| Idan kana da tsarki da aminci, Allah zai taimake ka, Ya maido da iyalin gidanka, ya yi maka sakayya. |
|
| 7 |
|
| Duk hasarar dukiyan nan da ka yi, ba kome ba ne In aka gwada da abin da Allah zai ba ka nan gaba. |
|
| 8 |
|
| “Ka tsai da zuciyarka a kan hikima irin ta zamanin dā. Ka kuma yi ta yin tunani a kan gaskiyar da kakanninmu suka koya. |
|
| 9 |
|
| Kwanakinmu 'yan kaɗan ne kawai, Ba mu san kome ba, Mu inuwa ne kawai a fuskar duniya. |
|
| 10 |
|
| Amma ka yarda masu hikima na zamanin dā su koya maka, Ka kasa kunne ga abin da za su faɗa. |
|
| 11 |
|
| “Iwa ba ta tsirowa inda ba ruwa, Ba a taɓa samunta a ko'ina ba sai a fadama. |
|
| 12 |
|
| In ruwan ta ƙafe, ita ce za ta fara bushewa, Tun tana ƙanƙana ba ta isa a yanke a yi amfani da ita ba. |
|
| 13 |
|
| Marasa tsoron Allah kamar iwan nan suke, Ba su da sa zuciya muddin sun rabu da Allah. |
|
| 14 |
|
| Suna dogara ga silin zare, murjin gizo-gizo. |
|
| 15 |
|
| Idan suka jingina ga saƙar gizo-gizo, za ta iya tokare su? Idan sun kama ta, za ta taimake su tsayawa? |
|
| 16 |
|
| “Mugaye sukan tsiro kamar ciyayi a hasken rana, Ciyayin da sukan yaɗu su cinye gona duka. |
|
| 17 |
|
| Saiwoyinsu sukan nannaɗe duwatsu, Su riƙe kowane dutse da ƙarfi. |
|
| 18 |
|
| Amma idan aka tumɓuke su, Ba wanda zai taɓa cewa sun kasance a wurin. |
|
| 19 |
|
| Hakika matuƙar murnar da mugaye suke da ita ke nan, Yanzu waɗansu ne za su zo su gāje wurarensu. |
|
| 20 |
|
| “Amma daɗai Allah ba zai rabu da amintattu ba, Ba kuwa zai taɓa taimakon mugun mutum ba. |
|
| 21 |
|
| Zai sāke barinka ka yi dariya ka ƙyalƙyata kamar dā, Ka kuma yi sowa da murna matuƙa. |
|
| 22 |
|
| Amma zai sa maƙiyanka su sha kunya, Za a shafe gidajen mugaye.” |
|
|
|
|