|
| 1 |
|
| Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa, |
|
| 2 |
|
| “Har yaushe za ka gama faɗa waɗannan abubuwa? Maganganunka ba su da amfani. |
|
| 3 |
|
| Allah ba mai shari’ar gaskiya ba ne? Ko Maɗaukaki yakan yi abin da ba daidai ba? |
|
| 4 |
|
| Lokacin da ’ya’yansa suka yi masa zunubi, yakan bar su su sha wahalar da zunubi yake kawowa. |
|
| 5 |
|
| Amma in za ka dubi Allah ka roƙi Maɗaukaki, |
|
| 6 |
|
| in kai mai tsarki ne, kuma mai adalci, ko yanzu ma zai taimake ka, yă mayar maka iyalinka da farin cikinka. |
|
| 7 |
|
| Ko da yake za ka fara da kaɗan, duk da haka za ka gama da samu mai yawa. |
|
| 8 |
|
| “Tambayi na gaba da kai ka ji abin da iyayenka suka koya |
|
| 9 |
|
| gama jiya kaɗai aka haife mu ba mu san kome ba, kuma kwanakinmu a duniya masu wucewa ne. |
|
| 10 |
|
| Ba za su bishe ka su kuma gaya maka abin da za ka yi ba? Ba za su yi magana daga cikin hikimar da suke da ita ba? |
|
| 11 |
|
| Ko kyauro zai iya yi girma a wurin da ba ruwa? Ko za tă taɓa iya yin girma ba tare da ruwa ba? |
|
| 12 |
|
| Yayinda take girma ba a yanka ta, takan mutu da sauri fiye da ciyawa. |
|
| 13 |
|
| Abin da yake faruwa ke nan da duk wanda yake mantawa da Allah; waɗanda ba su da Allah, ba su da bege. |
|
| 14 |
|
| Abin da yake dogara a kai ba shi da ƙarfi; abin da yake dogara a kai yanar gizo ce. |
|
| 15 |
|
| Ya jingina ga yanar gizo, amma ba ta tare shi, sun kama ta, amma ba za tă taimake su tsayawa ba. |
|
| 16 |
|
| Yana kama da shukar da aka ba ta ruwa sosai lokacin da akwai rana sosai, tana yaɗuwa da kyau; |
|
| 17 |
|
| shukar tana bin yaɗuwa, jijiyoyinta suna nannaɗe duwatsu, suna neman wurin da za su kama sosai a cikin duwatsu. |
|
| 18 |
|
| Amma lokacin da aka tuge shukar daga wurin da take, wurin ba zai san da ita kuma ba, wurin zai ce, ‘Ban taɓa ganin ki ba.’ |
|
| 19 |
|
| Ba shakka shukar ta mutu ke nan, kuma waɗansu za su tsiro a wurin. |
|
| 20 |
|
| “Ba shakka, Allah ba ya ƙin marar laifi, ko kuma yă ƙarfafa masu aikata mugunta. |
|
| 21 |
|
| Sai dai yă cika bakinka da dariya, yă sa ka yi sowa ta murna. |
|
| 22 |
|
| Maƙiyanka za su sha kunya, za a kawar da tentin mugaye.” |
|
|
|
|