|
| 1 |
|
| Ayuba ya amsa. |
|
| 2 |
|
| “Ai, na taɓa jin waɗannan duka, Amma ta ƙaƙa mutum zai yi jayayya da Allah har ya yi nasara? |
|
| 3 |
|
| Ta ƙaƙa za ka iya jayayya da shi? Yana yiwuwa ya yi maka tambayoyi guda dubu Waɗanda ba wanda zai iya ba da amsarsu. |
|
| 4 |
|
| Allah mai hikima ne, mai iko, Ba wanda zai iya ja in ja da shi. |
|
| 5 |
|
| Yakan kawar da manyan duwatsu farat ɗaya, Ya hallaka su da fushinsa, |
|
| 6 |
|
| Allah yakan aiko da girgizar ƙasa, ya girgiza duniya, Yakan jijjiga ginshiƙan da duniya take zaune a kansu. |
|
| 7 |
|
| Allah yana da iko ya hana rana fitowa, Ko kuma ya hana taurari haskakawa da dare. |
|
| 8 |
|
| Ba wanda ya taimaki Allah shimfiɗa sammai, Wanda yake taka raƙuman ruwan teku, ya kuma kwantar da su. |
|
| 9 |
|
| Allah ya rataye taurari a sararin sama, Wato su mafarauci da kare da zomo, Da kaza da 'ya'yanta da taurarin kudu. |
|
| 10 |
|
| Ba shi yiwuwa mu gane manyan abubuwa da yake yi. Ayyukan al'ajabansa ba su da iyaka. |
|
| 11 |
|
| “Allah yana wucewa kusa da ni, Amma ba na ganinsa. |
|
| 12 |
|
| Yakan ɗauki abin da yake so, ba wanda yake hana shi, Ba wanda yake tambayarsa cewa, ‘Me kake yi?’ |
|
| 13 |
|
| “Allah ba zai huce fushinsa ba. Ya murƙushe maƙiyansa waɗanda suka taimaki dodon ruwan nan da ake kira Rahab, wanda ya tayar masa. |
|
| 14 |
|
| To, ƙaƙa zan yi in samo kalmomin da zan amsa wa Allah? |
|
| 15 |
|
| Ko da yake ba ni da laifi, Duk da haka iyakar abin da zan iya yi ke nan, In roƙi Allah ya yi mini jinƙai, Shi da yake alƙalina. |
|
| 16 |
|
| Amma duk da haka ko ya yardar mini in yi magana ma, Ban yi tsammani zai saurare ni ba. |
|
| 17 |
|
| Shi ya aiko da hadura, suka yi kacakaca da ni, Suka ƙuƙƙuje ni, ga shi kuwa, ba wani dalilin da ya sa ya yi mini rauni. |
|
| 18 |
|
| Ya hana ni in ko shaƙata, Ina jin haushin dukan abin da yake yi mini. |
|
| 19 |
|
| In gwada ƙarfi ne? To, a iya gwada wa Allah ƙarfi? In kai shi ƙara ne? Wa zai sa shi ya je? |
|
| 20 |
|
| Ni ba ni da laifin kome, amintacce ne ni, A kunne sai a ji kalmomina kamar na marar gaskiya ne. Kowane abu da na fāɗa, kā da ni yake yi. |
|
| 21 |
|
| Ba ni da laifin kome, amma ba na ƙara damuwa. Na gaji da rayuwa. |
|
| 22 |
|
| Don haka ban damu da kome ba. Da marar laifin da mai laifin duk, Allah zai hallaka mu. |
|
| 23 |
|
| Sa'ad da marar laifi ya mutu farat ɗaya, Allah yakan yi dariya. |
|
| 24 |
|
| Allah ya ba da duniya ga mugaye, Ya makantar da dukan alƙalai, Idan ba Allah ne ya yi haka nan ba, to, wa ya yi? |
|
| 25 |
|
| “Kwanakina suna shuɗewa da sauri, ba mai kyau ko ɗaya. |
|
| 26 |
|
| Raina na wucewa kamar jirgin ruwa mafi sauri, Da sauri ƙwarai kamar juhurma ya kai wa zomo sura. |
|
| 27 |
|
| Idan an yi murmushi, Ina ƙoƙari in manta da azabata, |
|
| 28 |
|
| Sai dukan wahalar da nake sha ta yi ta firgita ni, Na sani Allah ya ɗauke ni mai laifi. |
|
| 29 |
|
| Tun da yake Allah ya ɗauka, ni mai laifi ne, To, me zai sa in damu? |
|
| 30 |
|
| Ba sabulun da zai iya wanke zunubaina. |
|
| 31 |
|
| Allah ya jefa ni a kwatami, Har tufafina ma suna jin kunyata. |
|
| 32 |
|
| Da a ce Allah mutum ne, Da sai in mayar masa da magana, Da sai mun je ɗakin shari'a a yanka mana shari'a. |
|
| 33 |
|
| Amma ga shi, ba wanda zai shiga tsakaninmu, Ba wanda zai shara'anta tsakanina da Allah. |
|
| 34 |
|
| Ka daina hukunta ni, ya Allah! Ka daina razanar da ni. |
|
| 35 |
|
| Ba na jin tsoro, Zan yi magana, domin na san zuciyata.” |
|
|
|
|